Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Ali Haruna Makoda, da wasu Kwamishinoni uku da suka sanar da ajiye aikinsu, da su koma bakin aiki.
Umarnin Gwamnan na cikin wata sanarwar da Kakakinsa, Malam Abba Anwar ya fitar ranar Talata.
- Sanatan da ke wakiltar mazabar Buhari a Majalisar Dattawa ya koma PDP
- Tsohon na hannun daman Buhari Solomon Dalung ya fice daga APC
Sai dai sanarwar ta ce Ganduje ya amince da ajiye aikin Kwamishinoninsa guda shida.
Daga cikin Kwamishinonin da Gwamnan ya mince da ajiye aikin nasu akwai Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo da Ibrahim Abubakar Karaye da Mahmud Muhammad Santsi da Muntari Ishaq Yakasai da Musa Iliyasu Kwankwaso da kuma Kabiru Ado Lakwaya.
Sanarwar ta ce, “Gwamnan ya gode musu kan matukar gudunmawar da suka bayar wajen hidimta wa Jihar, tare da yi musu fatan alheri a nan gaba.
“Ya kuma umarci Manyan Sakatarorin ma’aikatun da lamarin ya shafa da su karbi ragamar tafiyar da su nan take.
“Sai dai Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati [Ali Haruna Makoda] da dukkan sauran Kwamishinoni za su ci gaba da aiki,” inji sanarwar.
Daga cikin Kwamishinonin da Gwamnan ya umarta su koma bakin aiki akwai na Ilimi, Sanusi Sa’id Kiru da na Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Nura Muhammad Dankade da na Lafiya, Aminu Ibrahim Tsanyawa.
Idan za a iya tunawa, ko a kwanakin baya dai, Gandujen ya ki amincewa da takardar ajiye aikin Shugaban Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA), Baffa Babba Dan-Agundi.