✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Fastocin takarar Osinbajo da Ganduje sun bayyana a Kano

An dai lillika hotunan ne a wasu muhimman wurare da ke birnin.

Fastocin da ke alamta cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje za su tsaya takarar Shugabancin Kasa da ta Mataimaki a 2023 sun bayyana a wasu sassan Jihar Kano.

Fastocin da ke dauke da hotunan nasu dai na dauke da rubutu ‘Osinbajo-Ganduje Alliance (OGA)’, ‘For Better Nigeria’ da kuma ‘OGA Na Master’, kuma an lika su ne wasu muhimman wurare da ke Jihar.

Hotunan sun bayyana ne a karshen makon da ya gabata, a daidai lokacin da manyan baki da ’yan siyasa suka je Jihar don taron daurin auren dan Shugaban Kasa, Yusuf Buhari da ’yar Sarkin Bichi, Zahra Bayero da kuma bikin ba Sarkin sandar mulki.

Daga cikin wuraren da aka ga hotunan akwai titin da ke zuwa filin jirgin saman Kano, wato Airport Road, da kuma kan titin zuwa Katsina, wanda ta nan ne ake zuwa garin Bichi.

Kazalika, an ga fastocin nasu a wurare kamar titin Ahamdu Bello Way da na Murtala Muhammad da shate-talen titin Kano Club da dai sauransu.

Masu lura da al’amuran siyasa dai na harsashen cewa akwai yuwuwar mutum biyun su tsaya takara musamman idan takarar Bola Tinubu da Gandujen bat a kai ga gaci ba.

Shugabannin kungiyar magoya bayan kawancen, Oluleke Moses da Bello Adamu Mohammed sun shaidawa manema labarai cewa sun amince da takarar ne don samun hadin kai da ingantacciyar Najeriya.

“Mun yi amanna da cewa idan har mulki zai koma Kudu, to Osinbajo ne ya fi dacewa don ya hada kan kasar, domin kawo sauki da kuma gyara al’amura.

“Mun kuma yarda da cewa irin abubuwan da Ganduje ya yi a matsayinsa na Gwamnan Kano za su sa shi ya zama mafi dacewa da takarar Mataimakin Shugaban Kasa ga Osinbajo, kuma zai ci gaba da kare muradun Arewacin Najeriya da ke fama da talauci da rashin tsaro,”inji su.

Aminiya ta ruwaito cewa har yanzu dai Farfesa Osinbajo da Gwamna Ganduje ba su nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023 a hukumance ba.

Jihar Kano dai na da matukar muhimmanci ga duk wanda yake son ya shugabanci Najeriya kasancewar ita ce Jihar da ta fi kowacce yawan jama’a a Najeriya.