Tsohon Gwamnan Jihar Abiya, kuma jigo a jam’iyyar APC mai mulki, Sanata Orji Uzor Kalu, ya gargadi jam’iyyar da cewa muddin ita ma ba ta kai takararta yankin Arewa maso Gabas ba, to sai ta riga rana faduwa.
Kalu na wadannan kalaman ne kwana daya bayan babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta zabi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin dan takararta na Shugaban Kasa a zaben 2023 mai zuwa.
- Daga taimako, ’yar Ukraine ta ‘kwace’ mijin ’yar Birtaniyar da ta ba ta masauki
- 2023: Ina nan ina jiranka mu fafata — Tinubu ga Atiku
Orji Kalu, wanda Sanata ne mai ci kuma Bulaliyar Majalisar Dattijai, ya kuma taya mutanen yankin na Arewa maso Gabas murna, wadanda ya ce sun kama hanyar samun shugabancin Najeriya.
Ya ce, “Da fatan ’yan Najeriya sun lura da abin da ma lura da shi jiya [Asabar], cewar yanzu ba zai yiwu APC ta tsayar da dan takararta daga Kudu ba, muddin ba so take ta yi wa kanta ritayar dole ba a siyasance.
“Ina kira ga Kwamitin Zartarwar APC na Kasa da ya shirya mika tikitin takararsu ga Arewa maso Gabas.
“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na da damar zabar wanda zai gaje shi, kuma ina kira gare shi da ya zabi Sanata Ahmad Lawan, Shugaban Majalisar Dattijai.
“Hakan shi ne zai zama adalci ga mutanen yankin. Idan aka yi haka, ka ga ke nan an kusa kammala samun yanayin da kowacce daga cikin shiyyoyin siyasar kasar nan za ta samar da Shugaban Kasa.
“Ya zuwa yanzu, ya kamata dukkan sauran ’yan takara su ajiye aniyarsu, su mara wa dan Arewa maso Gabas baya. Sanata Ahmad Lawan ne kuma ya fi cancanta,” inji Orji Kalu.
Rabon yankin Arewa maso Gabas da shugabancin Najeriya dai tun tsakanin shekarun 1960 zuwa 1966, lokacin da Abubakar Tafawa Balewa ya zama Firaministan Najeriya.