✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Dan Barde ya zama dan takarar Gwamnan Gombe a PDP

Hakan na nufin shi zai tsaya wa jam'iyyar takarar Gwamna a Jihar a 2023

Sakamakon zaben fid da gwani na Gwamnan Jihar Gombe a jam’iyyar PDP wanda ’yan takara shida suka fafata, ya nuna cewa Muhammad Jibrin Dan Barde ne ya lashe shi.

Hakan dai na nufin shi ne zai tsaya wa jam’iyyar takara a zaben 2023 mai zuwa.

Dan Barde ya ka da abokan takarar tasa su biyar, cikinsu har da Dokta Jamilu Isyaku Gwamna da ya samu kuri’a 119.

 

Sauran ’yan takarar da suka sha kaye sun hada da Dokta Abubakar Ali Gombe da ya samu kuri’a 17 da AVM Adamu Fura ya samu kuri’a 18, Alhaji Ya’u Gimba ya samu kuri’a taya tilo da kuma Dokta Babayo Ardo Kumo ya samu kuri’a 13.

Nan take dai ’yan takarar suka rungumi Jibrin Dan Barde suna taya shi murna.