✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Buhari ya gana da Tinubu a Aso Rock

Tinubu ya ziyarci Shugaba Buhari a fadarsa da ke Villa a Abuja.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin mai neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa da ke Abuja.

Sai dai ba a bayyana wa manema labarai dalilin ganawar tasu ba, amma Aminiya ta gano cewa tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya ziyarci Buhari ne domin su tattauna wasu muhimman batutuwa sakamakon ya tafiyar da ya yi zuwa Kasa Mai Tsarki a lokacin da shugaban kasar ya gayyaci masu neman takarar kujerar shugaban kasa na APC da shugaban jam’iyyar, Sananta Abdullahi Adamu shan ruwa.

A lokacin da taron ya gudana, Tinubu ya tafi Kasar Mai Tsarki don gudanar da aikin Umrah, don haka bai samu damar halartar ba.

Amma Tinubu ya samu damar halartar liyafar da Buhari ya shirya a ranar 24 ga watan Maris, kafin babban taron APC na kasa.

Wasu na ganin ziyarar ta Tinubu na da alaka da neman Shugaba Buhari ya goya mishi baya kan takararsa ta neman zama magajinsa a kan kujerar shugaban kasa.

Sai dai Buhari ya yi wa dukkan masu neman takarar kujerar shugabancin Najeriya a APC dungu, inda ya ki fitowa ya bayyana goyon bayansa ga kowa daga cikinsu.