✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Babu dan Najeriyar da ya san ciwon kansa da zai zabi APC – Gwamnan Bayelsa

Ya ce APC ta nuna bai kamata a sake amince mata ba

Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya ce babu wani mai kaunar Najeriya wanda ya san ciwon kansa da zai zabi jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya ce sam jam’iyyar ba ta taka rawar gani ba a tsawon shekaru takwas din da ta kwashe tana mulki, don haka bai kamata a sake ba ta dama ba.

Diri, wanda yake jawabi ga mutanen mazabarsa lokacin da suka kai masa ziyara a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Yenagoa ranar Asabar, ya ce zabar APC a Jihar daidai yake da goyon bayan tabargazar da ake yi a matakin tarayya.

Sai dai ya roki mutanen jihar da su zabi ’yan takarar jam’iyyar PDP don tabbatar da ta samu gagarumar nasara a zaben mai zuwa.

Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, ya wakilta, ya ce kamun ludayin APC a tsawon shekara takwas ya nuna sam bai kamata a sake amincewa da ita ba.

Tun da farko da yake nasa jawabin, Shugaban kungiyar, Ogidi Bara Ben ya ce sun gamsu da nasarorin da gwamnati mai ci a jihar ta samu, musamman a aikin gina hanyar tsakiyar Jihar.