✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Babu adalci a tsarin karba karba – Sheikh Jingir

Ya ce sam babu adalci a tsarin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa

Shugaban Majalisar Malamai, na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah ta Kasa (JIBWIS) Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya ce sam, babu adalci a tsarin siyasar kasar na karba-karba tsakanin Kudanci da Arewaci.

Malamin ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen wani taron kara wa juna sani na kasa karo na 29 da kungiyar Izalar ta shirya a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Ya ce, “Za mu nuna wa duk wanda yake son ya yi tsarin karba-karba da mu cewa bai isa ba, ta hanyar amfani da kuri’unmu”.

Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga jama’a da su fito su yi rajistar zabe don dakile shiri na tsarin karba-karba da wasu ’yan siyasa suke kokarin kawowa.

“Jama’a gari ya waye, don haka don girman Allah muje mu yi kuri’a domin mu kare kanmu daga munafuncin tsarin karba-karba, ta hanyar zabar shugabanni da za su yi mana adalci,” inji Sheikh Jingir.

Shi ma a nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar malaman reshen Jihar Yobe, kuma mai bai wa Gwamnan Yobe shawara kan Harkokin Addini, Ustaz Babagana Malam Kyari, cewa ya yi kyakkyawan shugabanci ba ya samuwa sai an sami shugaba mara tsoro da kwadayi wanda kuma yake tausayin wadanda yake shugabanta.

Ya ce duk adalcin shugaba, idan bai sami mataimaka nagari ba, ba zai sami nasara ba.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da addu’ar samun shugabanni na gari a zaben shekara ta 2023 mai zuwa.