Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, kuma jigo a Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya ce ba za ta yiwu a mika wa Kudu takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar a zaben 2023 saboda son kai ba.
Ya bayyana haka ne yayin hira da BBC Hausa, inda ya ce ba laifi ba ne idan an yi hakan saboda tunanin zaman lafiya da kuma son farfado da tasirin jam’iyyar a Arewa, wadda ake sa ran za ta karbi mukamin shugabancin jam’iyyar.
- Najeriya na dab da fuskantar karancin iskar da mutane ke shaka – Masani
- Babban basaraken Jihar Taraba ya mutu
“Idan ma haka ta tabbata, sai dai a yi saboda zaman lafiya, misali akwai wadanda suke cewa yanzu PDP ba ta da karsashi a Arewa, don haka akwai bukatar a samu wani daga yankin da aka tabbatar da sahihancinsa a ba shi takarar Shugaban Kasa don farfado da tasirinta. To idan an yi haka ba laifi ba ne, amma idan aka ce dole sai a kai Kudu, to wannan ba za ta yiwu ba,’’ inji shi.
Ya kara da cewa “Ai an taba yin haka a PDP, aka dauko Obasanjo aka ce shi kadai zai yi takara, amma ka ga ai ba dole aka yi wa mutane ba, an yi ne domin ci gaban kasa da son tabbatar da zaman lafiya da karuwar arziki.’’
Da alama tsugune ba ta kare ba kan matsayar da Kwamtin Gwamnan Jihar Enugu, Mista Ifeanyi Ugwuanyi da Jam’iyyar PDP, suka dauka cewa za a mika shugabancin jam’iyyar zuwa Arewa.
Tuni dai wadansu daga cikin kusoshin jam’iyyar suke kalubalantar matakin inda suke ganin an shirya wa yankin makarkashiya ce don mayar da takarar Shugaban Kasa yankin Kudu a shekarar 2023.
A wani taron da gwamnonin Kudu suka gudanar a watan Yuli, sun ce dole shugabancin kasa ya kasance na karbakarba daga Arewa zuwa Kudu, kuma suna son Shugaban Kasar da za a zaba a 2023 ya fito daga Kudu saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.
Wannan batu ya janyo zazzafar muhawara a kasar nan, inda Kungiyar Dattawan Arewa ta ce babu wanda zai tilasta wa al’ummar yankin ta zabi wani dan takarar Shugaban Kasa da ya fito daga Kudu a zaben 2023.
Kakakin Kungiyar Dattawan Arewar, Dokta Hakeem Baba- Ahmed ya shaida wa BBC cewa Arewa tana da yawan masu zabe, don haka “Yankin ba ya shakkar kowace irin barazana.”