Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta nesanta kanta da labarin da ke yaduwa cewa ta saya wa tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, fom din takara a jam’iyyar APC.
Kungiyar ta ce ba ta siya wa wani dan takara fom ba kuma ba ta da aniyar yin hakan a nan gaba.
- Shekara daya bayan haduwa, matashi ya yi wa ‘kawar Facebook’ fyade
- Gudun yin sata ne ya sa na shiga sayar da Wiwi – Matashi
A cewarta, da ta siya wa wani dan takara fom gara ta karkata akalar kudin zuwa iyalan ’yan uwansu da ake kashewa da sacewa shanu a Kudu maso Gabashin da sauran sassan Najeriya.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun Sakatarenta na kasa, Baba Othman Ngelzarma inda ta ce ba ta alfanun siyan fom din ga kungiyar tasu ba, domin ita ma tana cikin bukatarsu.
Miyetti Allah Kautal Hore ta ce al’umma su duba yadda mambobinta ke fama da talauci sanadiyar ta’addanci da satar shanu ba dare ba rana da wasu bata-gari da ke kiran kansu da kungiyar tsaro ta ’yan sa-kai ke yi.
“Harkar siyasa ta ’yan siyasa ce, don ba mu ga amfanin goya wa wani dan siyasa baya ba bayan muna fama da kanmu a matakin kasa baki daya, sai dai idan har sun duba manufofinsa sun ga mai kawo musu sauki ne,” inji sanarwar.
A karshe kungiyar ta ce akwai bukatar al’umma su dinga bambamce Miyetti Allah da sauran kungiyoyin Fulani.