Wani masanin Kimiyyar Siyasa ya yi gargadin cewa ba lallai ne a iya gudanar da zabe a wasu sassa na jihohin Arewa maso Yamma ba saboda bullar wata sabuwar kungiya mai yada akidun da suka fi na ’yan bindiga hatsari.
Farfesa Abubakar Siddique Mohammed, wanda malami ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ne ya bayyana hakan a lakcarsa yayin bikin cika shekara 72 da kafa jam’iyyar NEPU a Kano ranar Litinin.
- An kashe kwamandan Taliban na Pakistan a Afghanistan
- Yadda Aka Biya N50,000 don Kallon Wasan Kwaikwayon Sarki Sunusi A Legas
Farfesan, wanda kuma shi ne Daraktan Cibiyar Bincike da Bunkasa Dimokuradiyya (CEDDERT) da ke Zariya, ce yanzu haka wannan kungiyar ce ke iko da wasu sassa na jihohin.
Masanin ya ce kungiyar na da sansanoni a yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna da Dandume a jihar Katsina, kuma tuni ta ci gaba da yada akidunta na kada a yi duk wasu harkokin siyasa.
Ya ce, “Yanzu haka, akwai wata kungiya da ta fi ta ’yan bindiga hatsari da ta bulla a wasu jihohin Arewa maso Yamma. Yanzu haka su suke iko da wani sashe na jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da wani bangare ma a jihar Neja.
“Sun haka duk wani nau’i na hada-hadar siyasa, kuma suna kokari su kwace yankunan daga karkashin gwamnati.
“Wannnan kungiyar ta fi ta ’yan bindiga hatsari saboda su ’yan bindiga basu da akida sai dai su kashe mutane su sace wasu su karbi kudin fansa. Amma wadannan mutanen tuni sun fara yada akidarsu tare da hana duk wata harka ta siyasa. Tsorona shi ne idan aka tafi a haka, ba lallai ne ma a iya yin zabe a cikinsu ba,” inji shi.
Da ya juya kan makasudin taron kuwa, ya ce tsohuwar jam’iyyar NEPU ta shimfida gwagwarmayar kwato wa talakawa hakkinsu duk da irin wahalar da suka sha daga gwamnatoci masu mulki a lokacin.
Shi ma da yake jawabi tun da farko, Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce an shirya taron ne don tunawa da ranar da aka kafa NEPU, wato ranar takwas ga watan Agustan 1950.
Farfesa Abbas wanda Mataimakinsa mai kula da bangaren karatu, Farfesa Sani Muhammed Gumel ya wakilta, ya kuma ce lakcar za ta taimaka wajen dabbaka akidun NEPU da PRP da ma na wanda ya kirkire su, Malam Aminu Kano.
Sai dai ya koka cewa kusan dukkan jam’iyyun Najeriya na yanzu ba a kan manufa aka kirkire su ba kuma su da wani cikakken tsari.