✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019: Zabe ne tsakanin mai tallar tsiya da mai tallar arziki – Bafarawa

Zabe ne tsakanin karya da gaskiya – El-Rufa’i   Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce zaben Shugaban Kasa na badi zai…

  • Zabe ne tsakanin karya da gaskiya – El-Rufa’i

 

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce zaben Shugaban Kasa na badi zai gudana ne a tsakanin mai tallar tsiya da mai tallar arziki, don haka ya rage ga masu zabe su zabi mai arziki ko matsiyaci.

Alhaji Attahiru Bafarawa Garkuwan Sakkwato ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin kaddamar da kamfe din dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar na jihohin Arewa maso Yamma da aka gudanar a filin sukuwa na Shehu Kangiwa da ke Sakkwato a ranar Litinin da ta gabata.

Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce ba zan yi dogon jawabi ba, “Amma mutanen Arewa maso Yamma kun fitar da mu kunya, kun nuna akwai PDP a wannan yanki. Mutum biyu ke tafiya, da mai tallar tsiya da mai tallar arziki, wa za ku bi; mai arziki ko matsiyaci? Mun san ba wanda ke bayar da mulki sai Allah. Da yardarSa dan takararmu Atiku Abubakar ne zai samu nasara kuma PDP za ta yi nasara daga sama har kasa. Za mu ci gaba da bayar da goyon bayanmu ga samun nasarar wannan tafiyar,” inji shi.

Bayan kammala zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP da ya bai wa Alhaji Atiku Abubakar nasara, an rika yada jita-jitar cewa abokan takararsa daga Arewa da dama za su yi masa kafar ungulu, inda aka rika bayar da misali da Sanata Ahmed Makarfi da Alhaji Sule Lamido da Alhaji Attahiru Bafarawa da kuma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, to amma  ganinsu a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyarsu, Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamwa bai ba wa mutane mamaki ba; ganin siyasa ta gaji haka.

A zantarwarsu da Aminiya a a wurin taron Sanata Ahmed Makarfi ya ce, “Mu duka wadanda suka yi takarar neman wannan tikiti na tsayawa takarar Shugaban Kasa tare da Alhaji Atiku Abubakar, muna goya masa baya dari bisa dari, muna tare da shi don a samu nasara. Wannan shi ne hadin kan da ake bukata, jam’iyyar da ba hadin kai ba jam’iyya ba ce. Ka ga APC ba ta da hadin kai, mu mun yarda da hukuncin Ubangiji, mun amince da duk wanda ya samu nasara za mu mara masa da jam’iyyarmu.”

“Muna tare da Atiku don mun yi imani abin da zai yi shi ne za mu yi, musamman a wannan yanki namu na Arewa maso Yamma,” inji shi.

Ya ce ya kamata a dubi abin da ke faruwa a jihohin Zamfara da Sakkwato da Kaduna da Katsina. “Ba za ka iya fita daga Kaduna ka ce za ka tafi Abuja ba, yanzu a sace ka, kafin ka shiga gida a sace ka, ka tafi gona haka. Wannan abu dole mu kawo karshensa, zaman lafiya ya samu, a yi walwala da kasuwanci. Mulkin Wazirin Adamawa ne zai samar da wannan, ku kare kuri’unku amma kada ku taka doka. Allah Ya ba mu nasara,” inji shi.

Da wakilinmu ya tambayi Alhaji Sule Lamido cewa wadansu na ganin akwai rabuwar kai a tsakaninsu, sai ya ce “Mu da muka yi takara a PDP ba rabuwar kai tsakaninmu. In wannan kake nema sai a APC, su ne ba su da hankali, ka san mu mun san mece ce siyasa, muna yin ta ce a matsayin ra’ayi ba da wata manufa ta hauka kamar APC, ba” inji shi. Game da ko za su iya kawo canjin da Jam’iyyar APC ta kasa kawowa? Sai ya amsa da cewa: “Kai zan tambaya, abin da kake saye baya shekara hudu da suka wuce, yanzu kana iya sayensa da kudin da ba wani bambanci, haka ake so mu zauna? Mun zo ne mu gyara goben matasa, mu mun gama aikinmu amma akwai maganar bayanmu. ’Ya’yanmu masu mutunci da biyayya da zumunci da son zaman lafiya. An san mulkin PDP da APC tarihi ne a shafi biyu a siyasance. PDP zaman lafiya, zumunci, son juna da hadin kan jama’a. Shafin APC rashin zaman lafiya, sace mutane, Boko Haram da yunwa haram da sauran annoba a Najeriya. An ce jiki magayi, kowa guminsa ya dafa shi, in kun nuna kun yi hankali to ku yi zaben samun hakki, shi ne ku zabi babban yayanmu Atiku Abubakar Wazirin Adamawa, shi ne dan takararmu da za mu zaba. Shi dan asalin PDP ne, kayanmu ne, mallakarmu ne. Don haka ina kira ga ’yan Najeriya su zabe shi don ci gaban Najeriya,” inji Sule Lamido.  Game da zargi cewa ya ja baya a tafiyar PDP, domin an mayar da shi saniyar ware, Lamido ya ce: “Wannan magana ce kawai. Ni uba da uwa ne ga Jam’iyyar PDP. Ba ta yi min laifi ba, wadansu ne kawai ke fadin abin da babu don kawai su kawo cikas ga tafiyarmu. Tafiya daya ce muke yi cikin mutunci da sanin ya kamata, don muna son a gyara lamurran kasar nan da suka lalace a hannun APC. Duk wani batu marar kan gado ba shi ne gabanmu ba.”