A yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya halarci harabar rattaba hannun zaman lafiya akan zaben 2019, dan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar bai halarci zaman ba.
Kwamitin zaman lafiya na kasa ne ya shirya taron wanda tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ke jagoranta.
An dai shirya zaman rattaba hannun ne a dakin taro na ICC a Abuja. Yayin da shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus bai halarci zaman ba, kamar yadda aka tsara.