✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda PaywithSpecta ke kara wa ’yan Najeriya karfin yin sayayya

Gudunmuwarmu wajen karfafa tattalin arziki da wanzuwar cinikayya

Kwanan nan Bankin Sterling, babban mai ba da rance na zamani a Nijeriya, ya kaddamar da PaywithSpecta, hanyar ba da bashi ta intanet don kara wa ’yan Najeriya ikonsu na yin sayayyar yau da kullun.

Shugaban Sashen Kula Kwastomomi da Kasuwanci na Bankin, Shina Atilola, ya yi bayani kan sabuwar hanyar da kuma yadda hakan ke ba wa mutane damar yin muhimman sayayyan da biyan kudin makaranta da kudin asibiti da kadan-kadan, wanda kuma ke haifar da karin ciniki da bunkasa tattalin arzikin. 

A baya-bayan nan Bankin Sterling ya kaddamar da tsarin biya wa masu sayayya kudi a wurin ’yan kasuwa na PayWithSpecta, shin me tsarin ya kunsa?

COVID-19 ya shafi tattalin arzikin duniya da ma Najeriya, wanda kuma ya rage karfin aljihun mutane na biyan kudin abubuwan da suka saya.

Saninmu ne cewa dan kasuwa na so ya sayar da kaya, kwastomomi ma suna so su saya, amma babban kalubalen shi ne karfin aljihun mai bukatar kayan na yin sayayya.

Shi ya sa muka kirkiro PaywithSpecta don magance wannan matsalar ta yadda yake ba masu amfani da shi ikon biyan kudin sayayyar da suka yi a hankali, sannan su kuma ’yan kasuwar ya biya su nan take.

PayWithSpecta na samar wa masu amfani da shi isassun kudaden yin sayayyan mahimmanci abubuwa na yau da kullum. Ta bangaren yan kasuwa kuma, yana kawo musu cikini sosai. Ta haka, masu amfani da shi na iya biyan kudin kaya da ayyuka ba kamar da ba.

PaywithSpecta, an bullo da shi ne don ya karo wa ’yan kasuwa ciniki tare da samar wa kwastomomi damar mallakar abubuwan more rayuwa ba tare da sun wahala ba.

Me ya sa bankinku ya bullo da tsarin da mutane za su za su tafi da abin da suka saya gida daga shagunan ’yan kasuwa tare da zabin biyan na gaba?

Ka san yadda bullar cutar COVID-19 da dokar hana fita da aka sanya suka illata harkokin kasuwanci, musamman kananan yan kasuwa da iyalai, wanda kuma ya yi tasiri wajen tabarbarewar tattain arziki.

Hakan na nufin mutane ba za su iya yin sayayya ba, ’yan kasuwa kuma ba za su yi ciniki ba, masu masana’antu kuma sai dai su ajiye kayan da suka sana’anta a dakunan ajiya, sannan su daina yin sababbi.

Hakan zai haifar da sallamar ma’aikata da karuwar rashin aiki wanda kuma zai kara tsananin durkushewar tattalin arziki, saboda sayayyar da ake yi ta yau da kullum ce ke motsa ta kuma bunkasa tattalin arziki.

Shi ya sa muka bullo da PayWithSpecta a matsayin gudunmuwarmu wajen karfafa tattalin arziki da tabbatar da wanzuwar cinikayya da kuma kauce wa matsin tattalin arziki

Me ake bukata daga kwastomomi ko ’yan kasuwar da ke neman shiga wannan tsarin biyan kudin?

Abubuwan da ake bukata masu sauki ne. In dai dan kasuwa ne, bayanansa kawai ake bukata: Sunan kamfaninsa ko shagonsa da Lambar Rajistar Kamfanin (RC).

Da ya ba mu za mu sa shi a kan tsarin, daga nan kwastomomi za su fara sayen kayan da suke bukata a kantinsa.

Da sun tashi sayayya sai su halarci shagon, idan shagon na intanet ne, sai su ziyarci shafinsa su sayi abin da suke bukata; Sannan su biya da kudin intanet na PaywithSpecta.

Abokin cinikinmu da ke neman kudin intanet na PayWithSpecta kuma sunansa da lambar ajiyarsa zai bayar. Da su za mu yi amfani wajen tantance karfinsa sannan mu kayyade masa yawan kudin intanet da zai yi amfani da shi na tsawon wata uku.

Zai iya yin sayayya da su, cirar tsabar kudin ko kuma amfani da su ya yi sayayya a wurin ’yan kasuwar da ke karbar PayWithSpecta a cikin wata ukun.

Ana kuma iya biyan kudin makaranta ko kudin asibiti da PayWithSpecta. Misali, idan mutum ba shi da lafiya ko za a yi masa tiyata amma ba shi da kudi, zai iya biya da kudin intanet din.

 

Ta yaka ake iya gane karfin kwastoma kafin a kayyade mishi yawan kudin PaywithSpecta da za a ba shi?

Abu mai sauki! Idan ya ba mu sunansa da lambar ajiyarsa za mu iya samun bayanan asusun ajiyarsa na tsawon wata shida; Da haka za mu gano karfinsa, mu tura mishi rancen darajar kudin, gwargwadon karfin nasa.

Daga nan kuma shi zai yanke wa kansa shawarar nawa zai kashe daga kudin da aka ba shi bashin.

 

Shin darajar kudin intanet din kamar katin kudin intanet ne? Wadanne tsare-tsare ko fa’idodi na musamman ne PaywithSpecta ke da su?

Gaskiya ne. Bari in fara da abubuwan da PaywithSpecta zai dakatar. Yanzu kana da zabi idan za ka yi sayayya a shago kai tsaye ko ta intanet: Za ka iya biya da kati ko da PaywithSpecta.

Da zarar ka sanya lambar shaidarka da Specta ID, nan take za a ciri kudin kayan da ka saya, a sanya wa dan kasuwar nan take. Saboda haka ba batun daukar katuna da yawa, zuwa ciran kudi a POS ko daukar kudi.

Sannan an kawar barazanar wani ya tisa ka da karfin tuwa ya kai ka ATM ya tilasta maka sanya katinka da lambobinka na sirri ka ciri kudi

PaywithSpecta na da aminci, dadin sha’ani, sauri da saukin sayayya ko biyan kudi ga ’yan Najeriya.

 

Wane tasiri ake burin ganin tsarin ya yi a kan tattalin arziki?

Ga kwastomomi yana ba su damar cika burinsa ta yadda za su iya sayen mota, kayan gida, cefane da sauran muhimman abubuwa ba tare da lallai suna da kudin ba.

Sai dai su biya ta PaywithSpecta sannan a rika cirar kudin da kadan-kadan a tsawon lokaci daga wurinsu, wanda hakan ke habaka kasuwanci da shigar kudade hannun ’yan kasuwa.

A bangaren tattalin arziki kuma, yanzu muna cikin matsin tattalin arziki kuma sana’anta kaya ya ragu saboda yadda karfin aljihun mutane na yin sayayya ya rugu.

Idan ’yan kasuwa da kamfanoni ba sa samu su sayar da kaya matsalar za ta ci gaba wanda kuma za ta kai ga sallamar ma’aikata.

Amma idan d a PayWithSpecta, ’yan kasuwa sa su rika samun ciniki suna sayar da hajojinsu, masana’antu kuma za su kara yawan kayayyakin da suke samarwa.

Karuwar sana’anta kaya zai samar da karin ayyukan yi da karin kwastomomi masu karfin aljihu, wanda hakan zai bunkasa kasuwanci tare da farfado da tattalin arziki.

 

Samar da rance ga masu sayayya ya yi karanci a Najeriya ya yi karanci idan kaka kwatanta da manyan kasashe, ta wace hanya za a bukasa samun rance?

Wannan abu ne na al’ada. Yawanci abin da muka taso a kai shi ne tara kudi kafin mu sayi abin da muke so. Amma idan muka lura za mu ga mutane da kasashe mafiya arziki na duniya suna yawan amfani da bashi.

Sukan karbar bashi domin su zuba jari a harkokin kasuwanci da ke kawo bunkasar tattalin arziki.

Bankin Sterling, musamman Specta Team, shi ne kan gaba wajen jagorantar wannan sauyin. Za a  dauki lokaci, amma idan mutane suka ga irin fai’dojinsa wurin samun sayayya, za su bi sahu.

Muna kokarin ilimantar da jama’a da fadakar da su game da alfanun karbar rancen masu sayayya.

Misali, muna wayar da kan ’yan Najeriya game da abubuwan da za su iya saya su biya cikin watanni uku ba tare da biyan kudin ruwa ba.

Muna kuma sanar da su game da irin zabin ke suke da shi.

Ilimantar da masu sayayya na shi ne mabudin samun rancen masu sayayya. 

 

Shin wadanne irin nasarorin da Specta ya samu daga lokacin da aka fara shi a 2018?

Specta ya samu gagarumar nasara, muna kuma alfahari da shi. Ya ba da lamunin kusan biliyan N100 wanda kasa da kashi 1.5 na wadanda suka karbi rancen ne suka yi taurin bashi.

Muna alfahari da nasarorin da muka samu, kuma ba za mu dakata ba da kwazon da da ya kai ga kirkirar PaywithSpecta. 

Na san za ka yi mamaki din na ce ba mu riga mun kaddamar da shi ba, amma yanzu gwaji muke yi, sai  bana za mu kaddamar da shi baki daya.

Mun yi farin cikin ganin yadda mutanen suke tuturuwar rungumar sa da kuma yadda adadin ke ta karuwa. 

 

Wadanne matakai aka tanada don rage hadarin da ke tattare da masu taurin bashi?

A matsayinmu na banki, koyaushe muna kula da hadari. Dangane da PaywithSpecta, muna yin binciken kudi da tarihin bashin masu neman amfani da tsarin. Hakan na rage hadarin faruwar hakan.

Don haka, duk da cewa shiga tsarin na da sauri, ya kuma kunshi cikakken bayani.

Sannan baya ga tsarin na karbar kudi da aka saba, akwai tsarin bayar da umarnin biyan kudi (GSI), da kuma inshorar da ta dace. Saboda haka muna da natsuwa da ’yan kasuwa.

Hadarin bashi yana tasowa ne idan wadanda suka karbi bashi suka kasa biya ko ba sa so su biya, amma sanannen abu ne cewa yawancin kananan ’yan kasuwa da ke karbar bashin kasuwanci a shirye suke su biya.