✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Likitoci 113 suka kamu da coronavirus a Najeriya

Ministan lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire, ya ce likitocin kasar 113 ne suka kamu da cutar coronavirus. Ya ce, mafi yawa daga cikin likitocin da…

Ministan lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire, ya ce likitocin kasar 113 ne suka kamu da cutar coronavirus.

Ya ce, mafi yawa daga cikin likitocin da suka kamu suna aiki ne a asibitoci masu zaman kansu.

Dokta Ehanire, ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis, a yayin jawabin kwamitin yaki da cutar COVID-19 na gwamnatin tarayya ga manema labarai.

Ya kara da cewa, ba gaskiya ba ne maganar cewa likitoci 300 ne suka kamu da cutar a Najeriya, ”Su 113 ne kuma yawancinsu suna aiki ne da asibitoci masu zaman kansu ba ma’aikatan gwamnati bane.

“Kuma mun sha yin gargadin cewa coronavirus ba cutar da ake kula da ita a asibiti mai zaman kansa bane”, inji shi.

Ya ce kula da wadanda suka kamu da cutar ba aikin likitocin da ba su da horo na musamman a kan cutar bane.

”Su ke daukar cutar su kai ta gida, su sanya wa iyalansu, wannan abu sam bai dace ba, don haka duk ma’aikacin lafiyar da ba shi da horo, ba aikin sa bane kula da masu cutar”, inji shi.