Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) ta kama wani mutum ɗan shekara 85 bisa zargin lalata wata yarinya ’yar shekara huɗu a Jihar Nasarawa.
Lamarin ya faru ne a makon farko na watan Janairun 2025 a unguwar Kongo da ke Ƙaramar Hukumar Keffi ta jihar.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar NSCDC, Jerry Victor, ya ce babbar yayar yarinyar ce ta daga karar a lokacin da ta gano cewa karamar yarinyar na tafiya da ƙyar tare da kuma zubar jini daga kafafunta.
Victor ya yi zargin cewa mutumin ya yaudari ƙaramar yarinyar zuwa ne cikin dakinsa inda ya aikata hakan.
- An kama Lakurawa sun kai wa ’yan sanda sanda hanci
- ’Yan ta’adda sun ga harbi likita sace wasu a asibiti a Katsina
A cewarsa, ’yar uwar yarinyar ‘yar shekara huɗu ta nemi sanin hakikanin abin da ke damun ta, sai ta shaida mata cewa tsohon ya bata ta.
Ya ce, “abin takaici ya faru ne a unguwar Kongo da ke Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar. An kai rahoton lamarin ga hukumar NSCDC, inda nan take ta zage damtse kuma ta cafke wanda ake zargin mai shekaru 85 a duniya.”
Kakakin rundunar ya bayyana cewa gwajin da aka yi likita ya tabbatar da cewa an yi wa ƙaramar yarinya fyade.
Ya ce za a mika lamarin ga ma’aikatar shari’a ta jihar bayan bincike.
A zantawarsa da wakilinmu, wanda ake ya musanta tuhumar da ake masa.
Binciken da wakilinmu ya yi ya nuna cewa iyayen yarinyar da wadanda ake zargin maƙwabta ne.