✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

Bincike ya nuna wanda ake zargin ya jima yana safarar makamai a Jihohin Arewacin Najeriya.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta kama wani ɗan ƙasar Aljeriya, mai shekaru 58 kan zargin safarar makamai a iyakar Najeriya.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mohammed Dalijan ne, ya bayyana hakan a Gusau, a ranar Talata.

Ya ce ’yan sanda sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 16, yayin samame daban-daban da suka kai cikin makonni uku da suka gabata.

Hakazalika, sun samu wasu manyann bindigogi guda biyu da wata bindiga ƙirar gida daga hannun wani mai ƙera makamai a Jos, Jihar Filato.

Dalijan, ya ce rundunar ’yan sandan, bayan samun bayanan sirri, ta kama wannan mai ƙera makamai a Jos.

Ya ce sun bi sahun wani ɗan ƙasar Aljeriya da ke safarar makamai har suka kama shi a kan iyakar Illela.

“Wanda ake zargin ya amsa cewa ya daɗe yana safarar makamai tsawon shekara takwas.

“Yana sayar da bindiga a dukkanin jihohin Arewa maso Yamma. Lokacin da aka kama shi, an samu bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu a hannunsa,” in ji Dalijan.

Kwamishinan ya ƙara da cewa an kama wasu mutane da ake zargi, ciki har da masu kai wa ’yan bindiga babura.

Rundunar ta ƙwato harsasai, kuɗi Naira miliyan 2.5, da wasu kayayyaki daga hannun waɗanda ake zargin.

Har ila yau, ’yan sanda sun kama masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba tare da ƙwato injinan haƙar ma’adinai.

Dalijan, ya tunatar da jama’a cewa dokar hana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da Gwamnatin Tarayya da ta jihohi suka sanya har yanzu tana nan daram.