✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗalibar Jami’a ta rasu tana tsaka da wanka a Bauchi 

Tuni dai aka yi jana'izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Shugabannin Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi, sun tabbatar da rasuwar Naja’atu Salisu, ɗaliba a aji uku a fannin Kimiyyar Kwamfuta.

Rahotanni sun bayyana cewar an same ta cikin mawuyacin hali a banɗaki ɗalibai bayan ta je wanka.

Daraktan yaɗa labarai na ATBU, Zailani Bappa, ya tabbatar da lamarin, ya ce an kai Naja’atu asibitin jami’ar domin ba ta agajin gaggawa, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarta.

Bappa ya bayyana cewa, “Bayan lura da hakan, an garzaya da Naja’atu zuw Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa, inda likita ya tabbatar da rasuwarta. An birne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.”

Aminiya ta ruwaito cewar Naja’atu ta shiga banɗakin ɗalibai mata na kwalejin Gubi da safiyar Juma’a domin yin wanka ta kuma shirya ta tafi aji.

“Ta shirya kamar yadda ta saba domin zuwa ajin safe kafin ta shiga baɗakin wankan. Ta kawo kayan da za ta saka idan ta fito daga wankan, ta ajiye su a gefen gadonta,” a cewar abokiyar kwananta.

Haka kuma, a cikin sakon ta’aziyya, Kungiyar Ɗalibai ta ATBU, ta bakin Sakataren Ƙungiyar, Kwamared Danladi Zakiru, ta bayyana marigayiyar a matsayin ɗaliba mai ƙwazo wadda za a yi matukar kewarta a tsakanin ɗaliban jami’ar.