✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗaliban Kuriga: Halin da na shiga bayan sace ’ya’yana biyar —Mahaifiya

Ni da matata ba ma iya barci tun da aka sace mana da. Muna neman taimako.

Mutanen garin Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna da aka sace wa ’ya’ya a makon jiya sun ce suna cikin tashin hankali a duk lokacin da suka tuna ’ya’yan nasu da ke hannun barayin daji.

Akalla daliban makarantar firamare da sakandare 287 ne ’yan fashin dajin suka sace a ranar 7 ga Maris din nan kuma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto a babu labarin inda yaran suke.

Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin iyayen yaran inda suka ce a ranar da abin ya faru wasu daga cikin daliban ma ba su da koshin lafiya inda wasu kuma ko karin kumallo ba su yi ba suka tafi makarantar da safe.

Kasancewar yanayin zafi da ake ciki wasu iyayen suna ganin yaran za su yi matukar galabaita a cikin dajin domin da wuya su samu abinci da ruwan sha isasshe ballantana magani ga marasa lafiya.

Abin da ke damunsu shi ne har zuwa lokacin ’yan bindigar ba su tuntube kowa ba domin neman kudin fansa bayan sace su da suka yi wanda hakan ya kara jefa iyayen da sauran al’ummar gari a cikin damuwa.

Binciken Aminiya ya gano cewa babu wani gida a cikin garin Kuriga da lamarin bai shafa ba domin dukkan gidajen akwai dan gidan da aka sace.

Har ila yau daga cikin daliban akwai sama da ashirin wadanda marayu ne, wadanda dukkansu iyayensu sun rasu ne sakamakon ayyukan ’yan ta’addar a kauyen.

Bayan wannan hari kuma, kwasam sai ga barayin sun sake dawowa a daren Litinin inda suka tsaya da baburarsu a tsohuwar kwalejin da ke a wajen garin Kuriga.

Dole ya sa matasan garin suka sake fitowa domin kare garinsu inda wasu daga cikin mazauna garin suka nuna rashin gamsuwa da kalaman gwamnati da jami’an tsaro dangane da kokarin da suka ce suna yi wajen nemo yaran tun da har barayin sun sake dawowa kusa da garin.

Hajara Shu’aibu wacce aka sace wa yara biyar cikin kuka ta bayyana wa Aminiya cewa ba ta iya barci ballantana ta ci abinci.

A cewarta, ’ya’yanta biyar duka kanana ne domin daya daga cikinsu ko tafiya ba ta iya yi sosai hakan ya sa take cikin damuwa idan ta tuna halin da suke ciki.

“Ba na iya barci ballantana in ci abinci tunda aka sace min ’ya’ya biyar. Ji nake ma duniya ba ta da amfani a gare ni.

“Saboda haka ina kira ga gwamnati ta taimaka wajen karbo mana yaran nan duka,”in ji ta cikin hawaye.

Ita ma Fatima Kuriga wacce danta Suleiman ke cikin wadanda aka sace, ta ce tana cikin gida ta ji tashin bindiga ko da ta fita sai ta ji cewa ’yan fashin daji ne suka sace daliban makarantar.

“Dana Suleiman na cikin wadanda aka sace. Don haka muna kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta taimaka mana.

“Ba mu da abinci sannan kuma mazanmu ba sa kwana cikin gida da daddare domin suna fita aikin tsaro saboda barayin daji.

“Yanzu wadannan yara da aka sace suna cikin wani mawuyacin hali a cikin daji ba tare da abinci ko ruwan sha ba sannan ga zafin rana.

“Ko yaron da ya tsira daga hannun ’yan fashin har ya dawo mun ga halin da ya shiga a kwana guda.

“Ya shaida mana cewa a cikin rami ake ajiye su. Sannan ga shi ba mu da jami’an tsaro a Kuriga, amma mun ji abin da Gwamnan Jihar Kaduna ya fada, muna fatan Allah Ya ba shi ikon cika alkawarinsa,” in ji ta.

Ita kuwa Khadija Abdurra’uf ta ce tun bayan aukuwa lamarin a kullum tana kewar ’yarta Safiya Hassan inda ta roki gwamnati da ta taimaka wajen karbo su daga hannun wadannan mutane.

“Diyata Safiya Hassan tana rashin lafiya a ranar, amma ta tafi makaranta. Ba ta ma yi karin kumallo ba a ranar saboda kada ta makara,” inji ta.

A cewarta, matasan garin sun yi kokarin tunkarar ’yan fashin dajin amma saboda ba su da makamai suna ji, suna gani suka tafi da daliban.

Shi ma Shehu Lawal mahaifin daya daga cikin daliban mai suna Aminu mai shekara10 da haihuwa cewa ya yi ba ya iya barci.

“Ni da matata ba ma iya barci tun da aka sace mana da. Muna neman taimako, a karbo mana yaran nan domin mu samu kwanciyar hankali domin kuwa a yanzu ba ma jin dadin rayuwa.

“ Kusan dukkan yaran ba su yi karin kumallo ba suka tafi makaranta aka kuma sace su kuma yawancinsu kanana ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa a matsayinsu na iyaye suna cikin matukar damuwa saboda ba su san a wane hali suke ciki ba.

“Idan ka shiga gidajenmu sai ka zub da hawaye. Har yanzu ’yan fashin dajin ba su tuntube mu ba a kan maganar kudin fansa saboda akasarin yaran kanana ne ba su da lambar wayar da za su bayar.

“Kuma ba mu da kudin da za mu bayar ko sun kira saboda duk sun lalata mana gonakinmu. Don haka ko da sun bukaci kudi ba za mu iya biya ba,” in ji Lawal.

Shi kuma Malam Is’hak Kuriga daya daga cikin malamai a garin ya nuna alhininsa ne a kan halin da mutanen garin ke cikin tun bayan wannan lamari.

Ya ce kusan kowa na cikin damuwa saboda babu labarin inda yaran suke sannan ’yan fashin ba su kira ba.

Kuma ya ce babu wani yaro da ya dawo tun bayan daya da ya kubuta daga hannun ’yan fashin dajin a ranar da aka sace su.

“Dukkan yaran da aka sace babu wani yaro daga wajen Kuriga, duk yaran garin nan ne sannan iyayensu duk ’yan cikin Kuriga ne.

“Kuma har yanzu babu labarin inda suke,” in ji shi.

Malamin ya yaba wa jami’an gwamnati da suka ziyarci garin domin jajanta wa iyayen yaran inda ya ce fatansu shi ne a taimaka wajen karbo yaran domin hankalin kowa ya kwanta sannan a sama musu jami’an tsaro a garin domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kauyukan da ke zagaye da Kuriga sun watse Daya daga cikin mutanen garin Kuriga Lawal Kuriga ya shaida wa Aminiya cewa Kuriga na kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari ne kuma duka kananan garuruwan da ke kewaye da garin sun watse saboda matsa masu da ’yan fashin daji ke yi.

Ya ce hakan ya sa Kuriga ne kawai babban gari da ya rage a yankin duk da matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin.

A cewarsa Kuriga ba ta wuce kilomita 90 ba daga Kaduna sai dai rashin kyan hanyar mota.

“Akwai kauyukan da suke kewaye da Kuriga kamar Sarari, Unguwar Barau, Manini, Gauro, Tashar Tsuntsaye, Unguwar Rahama, Janmaye, Kufara, wadanda dukkansu a yanzu sun watse saboda ’yan fashin daji sun matsa musu.

“Inda kawai za ka samu ’yan mutane shi ne Rafin Masga.

‘Tsoronmu kada a tsallaka da yaran Zamfara’

Game da ko a ina suke ganin za a kai yaran da aka sace sai Lawal Kuriga ya ce suna tsammanin a yanzu suna dajin Kuriga zuwa Birnin Gwari ne.

“Sai dai muna tsoron kada a tsallaka dajin Birnin Gwari da yaran domin da sun yi hakan to labari zai canza domin yankin Dansadau a Zamfara za su shiga.

“Maganar da ake yi babu mai layin waya a cikin yaran domin kanana ne sannan sai dai fa idan ’yan fashin sun ga damar kiran waya za su kira, amma har yanzu ba su kira ba.

“Abin akwai tashin hankali sai dai mu roki Allah Ya kawo mafita,”in ji shi.

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya fadi a ranar da ya ziyarci garin cewa gwamnatinsa ta sha alwashin yin dukkan mai yiwuwa wajen karbo yaran.

Sai dai har yanzu a cewar mutanen garin suna jiran ganin gwamnatin jihar da ta tarayya sun cika alkawaransu na tabbatar da an kubutar da daliban baki dayansu daga hannun ’yan bindigar.