✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɓarawon mota ya shiga hannu a Abuja

Rundunar ta kama wanda ake zargin a wani otal da ke yankin Jabi.

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, sun kama wani mutum da ake zargi da ƙwace wata mota ta hanyar amfani da bindiga, watanni uku da suka wuce.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Benneth Igweh ne, ya bayyana hakan lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin a ranar Litinin.

Ya ce wanda ake zargin, mai suna Michael Uke, ya sace mota kirar Toyota Corolla mai lamba ABC 258 LD ta hanyar amfani da bindiga a ranar 2 ga watan Mayu, 2024, a kan hanyar Kuje.

’Yan sanda sun bi sahun sa har zuwa wani otal da ke yankin Jabi, inda suka same shi tare da motar da ya sace.

’Yan sandan sun kuma gano cewa wanda ake zargin ya sauya lambar motar zuwa AGD 146 JP.

A yayin bincike, sun gano na’urar POS, wuƙa, da kuma hular sojoji a wajensa.

’Yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Har wa yau, rundunar ta buƙaci mazauna yankin su riƙa sanar da su abubuwan da ke faruwa ta waɗnnan lambobin: 08032003913, 08028940883, 08061581938, da 07057337653.