✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙungiya ta yi watsi da buƙatar ɗauke cibiyar NCC daga Kano

Ƙungiyar ta ce Jihar Kano ne inda ya fi cancanta a bar cibiyar ta NCC.

Ƙungiyar Matasan Arewa ta yi watsi da kiran da ake yi na sauya wa Cibiyar NCC da aka lalata lokacin zanga-zangar yunwa matsuguni daga Jihar Kano zuwa Jihar Kebbi.

Wannan na zuwa ne biyo bayan lalata tare da sace kaya da ɓata gari suka yi a lokacin zanga-zangar yunwa a Kano.

Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wanda Dokta Aliyu Mohammed da sakatarenta Dokta Hafiz Bello suka sanya hannu, sun soki buƙatar sauya wa cibiyar matsuguni.

Sun bayyana hakan a matsayin “hanyar yaudarar mutanen Kebbi.”

Sanarwar ta ce sauya wa cibiyar matsuguni zuwa Kebbi abu ne mai kyau, amma hakan zai kawo jinkiri wajen cin moriyar cibiyar.

Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin gyara ɓarnar da aka yi wajen da Kano maimakon fara tunanin sauya matsuguni.

Ƙungiyar ta jaddada muhimmancin Jihar Kano a matsayinta ta Babbar Cibiyar Kasuwanci a Arewacin Najeriya.

Sun ce duba da irin tasirin da Kano ke da shi da kuma hanyoyin da ta ke da su wajen harkokin kasuwanci da kuma filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ta ke, zai fi kyau a bar cibiyar a can don cin moriyar matasan Arewa.

Sun roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya bayar da umarnin fara gyaran cibiyar.

Sanarwar ta kuma yi nuni da kiran da ake yi na sauya wa cibiyar matsuguni ba shi ne abin da ya dace ba, face duba da irin tasirin da Kano ke da shi a Najeriya.

Ƙungiyar ta ce hakan zai taimaka gaya wajen bunƙasa harkokin tattalin arziƙi a Arewacin Najeriya.

Ƙungiyar ta ce tabbas Jihar Kebbi, na buƙatar samun abubuwan more rayuwa, amma ta ce yana da kyau a yanzu a fi mayar da hankali kan bunƙasa harkar noman shinkafa wanda ya yi nisa a jihar.