✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙuncin rayuwar da ake ciki a Nijeriya ya misali — Abdulsalami

Rarraba wa ’yan Nijeriya kayayyakin rage raɗaɗi ba zai magance matsalar tsadar rayuwa ba.

Tsohon Shugaban Mulkin Soji a Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana damuwa kan matsi da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar da a cewarsa ya wuce gona da iri.

Dangane da hakan ne Janar Abdulsalami ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen wannan raɗaɗi da ake fuskanta a faɗin ƙasar.

Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce matakin da gwamnatin take ɗauka na rarraba wa ’yan ƙasa kayayyakin tallafin rage raɗaɗi ba zai magance komai ba la’akari da ƙolokuwar da tsadar rayuwa ta kai a ƙasar.

Janar Abdulsalami ya ce akwai wawakeken gibi a tsakanin talaka da masu jagoranci duba da cewa tazarar da ke tsakaninsu ta sanya muryoyin waɗanda ke koken damuwa ba su kaiwa kunnen da ya kamata a saurara.

Da yake jawabi yayin da wakilan wata ƙungiyar mai kare muradun dimokuraɗiyya da haƙƙin dan Adam su kai ziyara gidansa da ke birnin Minna a Jihar Neja, tsohon shugaban ƙasar ya zargi shugabannin Nijeriya da watsi da talakawan ƙasar ta yadda ba su sauraron koke kan halin matsin da suke jefa su a ciki.

Aminiya ta ruwaito wakilan ƙungiyar suna roƙon tsohon Shugaban Ƙasar da ya yi amfani da tasirinsa wajen janyo hankalin Shugaba Bola Tinubu kan kawo ƙarshen tsadar rayuwar da ya yi wa ’yan Nijeriya ɗaurin dabaibayi.

“Tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar ta wuce gona da iri. Babu wani ɗan Nijeriya da ba ya kokawa kan wannan ƙuncin a yanzu wanda a kullum abin yana ƙara ta’azzara.

“Saboda wannan yanayi da ake fuskanta a yanzu mutane ba su samun damar cin abinci sau uku a rana.

“Babu abin da bai gagari talaka ba a yanzu saboda tsadar sufuri da man fetur da ƙarin kuɗin makarantar ɗalibai alhali babu kuɗi a hannun jama’a,” a cewar Janar Abdulsalami.

Ya bayar tabbacin cewa kasancewarsa tsohon Shugaban Nijeriya, ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin shugabanni a kowane mataki sun tunkari waɗannan matsaloli domin magance su cikin lokaci taƙaitacce.

Ya buga misali da yadda wata ƙungiyarsu take faɗi-tashin bai wa gwamnati shawarwari musamman kan hanyoyin da za a rage wa talakawa raɗaɗi.

“Mun shaida wa gwamnati cewa rarraba kayayyakin tallafin rage raɗaɗi babu abin da zai magance idan aka yi la’akari da tsadar abinci da sauran kayayyaki.

“Mun bai wa gwamnati shawarar sayo kayan abinci sannan ta sayar wa ’yan ƙasa a farashi mai sauƙi.

Dangane da zanga-zangar tsadar rayuwa ta #EndBadGovernance da aka gudanar da kuma makamanciyarta da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar daga ranar 1 ga watan Oktoba, Janar Abdulsalami ya roƙi ’yan Nijeriya da su zama jakadun zaman lafiya a yayin da kuma yake kiran gwamnati da ta tabbatar da mutunta ’yan ƙasar ta hanyar ɗaukarsu da muhimmanci.