Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin maido da ƙananan yaran da aka gurfanar a wata kotu a Abuja zuwa Jihar Kano.
A bayan nan dai an riƙa cece-kuce dangane da bullar bidiyon wasu ƙananan yara da aka gurfanar a gaban wata kotu Abuja da aka kama tun yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a farkon watan Agusta.
- Jihohi 20 da suka fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi
- Yara masu zanga-zangar yunwa sun sume a kotu
A cikin bidiyon, wasu daga cikin ƙananan yaran sun suma a zauren kotun kan abin da ake fargabar cewa yunwa ta yi musu mummunar illa a tsawon lokaci da suka shafe a hannun mahukunta.
Sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Gwamna Yusuf ya umarci Kwamishinan Shari’a kuma Atoni-Janar na Kano, Barista Haruna Isa Dederi, da ya gaggauta tarar hanzarin lamarin domin dawo da yaran gida.
Bayanai sun ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da belin mutum 67 cikin 76 da Gwamnatin Najeriya ta zarga da cin amanar ƙasa sakamakon zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.
Kotun ƙarƙashin Mai Shari’a Obiora Egwuatu ta saka wa kowannensu sharaɗin naira miliyan 10, da kuma gabatar da mutumin da zai tsaya wa kowa, wanda ta ce dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnati mai matakin albashi na 15.
Sai dai mutum 27 cikin waɗanda aka gurfanar a kotun ƙananan yara ne da shekarunsu ba su kai 18 ba, har da ma mai shekara 14, kamar yadda takardun kotun suka tabbatar.
An tura manyan cikinsu zuwa gidan yari, an kuma aika da wasu yaran wani gidan kula da kangararrun yara har zuwa ranar 25 ga watan Janairu, inda za a ci gaba da shari’ar.
An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
An kama su ne a garuruwan Kano, da Katsina, da Gombe, da Abuja, da Jos, da Kaduna.