Ɗan Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, Ashraf Adam Lamido, ya auri masoyiyarsa, Sultana Nazif, ’yar fitaccen ɗan siyasa daga Jihar Bauchi, Sanata Suleiman Mohammed Nazif.
Auren ya gudana a Masallacin Ƙasa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
- Zanga-zanga: Babu wanda ya rasu a Katsina — ’Yan Sanda
- Zanga-Zanga: Dalilin da Gwamnan Kano yake ɗora wa ’yan adawa laifi — APC
Ƙanwar angon, Fulani Siddika ce, ta wallafa hotuna da bidiyon auren a shafin Instagram.
Manyan mutane da dama, ciki har da jami’an gwamnati da sarakunan gargajiya, sun halarci bikin.
Ga hotunan yadda bikin ya gudana: