Ɗan majalisar da ke wakiltar Mazaɓar Jema’a/Sanga a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga Jihar Kaduna, Hon. Daniel Amos, ya tallafawa fiye da mutane 3,000 daga mazaɓarsa da kuɗi kimanin Naira miliyan 400.
Yin tallafin wani ɓangare na rage raɗaɗin talauci da kuma inganta rayuwar jama’a.
Amos, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai da ke Kula da Ayyukan Majalisa, ya gudanar da wannan rabon tallafin ne a Ƙaramar Hukumar Sanga don murnar bikin cikarsa shekaru biyu a matsayin ɗan Majalisa.
- Dalilin da ya sa aka sauya sunan Jami’ar Maiduguri — Ma’aikatar Ilimi
- Dantata mutum ne mai tausayi da ƙaunar Najeriya — Tinubu
Da yake jawabi a wajen taron, ɗan majalisar ya bayyana cewa ya tallafawa jama’arsa ne don sauƙaƙa rayuwarsu da kuma taimaka wa jama’ar mazaɓarsa daga ɓangarori daban-daban, ciki har da ɗalibai da matasa maza da mata da shugabannin al’umma da kuma jami’an tsaro ba tare da la’akari da jam’iyyun da suka fito ba.
A cewarsa, mutane 3,000 ne suka amfana da Naira dubu 100 kowannensu, yayin da wasu mutum 100 suka karɓi Naira miliyan ɗaya kowannensu, lamarin da ya kai jimillar kuɗin ya kai Naira miliyan 400.
“Manufarmu ita ce rage wahalhalun da mata da yara ke fuskanta tare da samar da tubalin ci gaba da zai shafi kowa da kowa,” in ji Amos.
Haka zalika, ya bayyana cewa a cikin shekarar da ta gabata ya tallafa wajen gina rijiyoyin burtsatse guda 120 kowanne a ƙananan hukumomin Jama’a da Sanga, da samar da burtsatse mai amfani da hasken rana guda 25 da kuma dasa fitilun hanyoyi sama da 2,000 a sassa daban-daban na mazaɓarsa.
Amos ya tabbatar wa mutanen Jama’a ’a da Sanga cewa, zai ci gaba da cika alƙawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe domin amfanin kowa.
A nasa jawabin, Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Wakilai ta Ƙasa wanda shi ne ya jagoranci taron, Kingsley Ogunda Chinda ya bayyana Amos a matsayin shugaba abin dogaro wanda ya damu da walwalar jama’a, inda ya ce gudunmawarsa ta zarce mazaɓarsa domin suna alfahari da shi hatta a majalisa.
“Ɗan Amos abin alfahari ne ba ga mazaɓarsa ba kaɗai, har ma ga Majalisar Tarayya da ƙasa baki ɗaya. A madadin ’yan Majalisar Wakilai, muna gode wa al’ummar Jama’a ’a da Sanga bisa ba mu mutum mai hali nagari kamar Amos,” in ji Chinda.
Ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace tare da koyi da irin halin taimakon juna da Ɗan majalisar ke nunawa.
Sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron da suka haɗa da Mataimakin shugaban Marasa Rinjaye a Majalisa, Ali Isah; da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Nuhu Bajoga da wani jigo a Jam’iyyar APC, Tanko Rossi. Dukkansu sun yaba wa Amos bisa ƙoƙarinsa tare da bayyana shi a matsayin abin a zo a gani kuma ya zo a lokacin da ya dace.
Sannnan sun yi kira ga sauran ‘yan siyasa da masu hali su ɗauki irin wannan mataki na taimakon marasa ƙarfi.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana da wannan tallafi da suka tattauna da Aminiya sun bayyana godiyarsu ga ɗan majalisar, tare da cewa wannan tallafi na kuɗi zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa harkokinsu na kasuwanci.
Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Laraba, Daniel Amos ya raba tireloli biyu na taki, buhuna 3,000 na shinkafa da kuma baburan huɗu na adaidaita sahu a yankin na shi.