✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗalibai biyu sun mutu a turmutsutsun rabon kayan abinci a Nasarawa

Ɗalibai mata biyu sun riga mu gidan gaskiya a wajen karɓar rabon tallafin abinci a Jami’ar Jihar Nasarawa.

Aƙalla dalibai mata biyu na jami’an jihar Nassarawa da ke Keffi ne suka mutu sakamakon wani turmutsutsu da aka yi a wajen karbar kayan tallafi na gwamnati a dandalin taro na jami’ar da safiyar Juma’a.

Gwamnatin Jihar Nassarawa dai ta yi amfani da dandalin taron da ke jami’ar ne wajen raba kayan tallafin wahalar rayuwa ga daliban jami’ar.

Wani shaidar gani da ido ya ce, ɗaliban da suka rasu na daga cikin waɗanda suka yi tattaki zuwa wurin rabon kayayyakin domin su karɓi nasu kason.

“Abin da muke ji yanzu shi ne ɗalibai mata biyu sun rasu a dalilin rashin samun numfashi saboda cunkoson jama’a.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa reshen Jihar Nasarawa Yunusa Yusuf Baduku ya ce, an garzaya da akasarin ɗaliban da cunkoson ya rutsa da su zuwa asibitocin yankin domin duba da lafiyarsu.

A cewarsa, “Gaskiya abin da ya faru a safiyar yau a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, abin tausayi ne.

“Bayan shirin da muka yi na raba kayan agaji ga ɗaliban da za a yi a dandalin taro na Jami’ar, kwatsam sai ga wasu (ɗaliban) masu tarin yawa sun isa wurin kuma jami’an tsaro suka rasa yadda za su yi da su.

“Sun bi ta ƙofar shiga dandalin taron jami’ar inda za a raba buhunan shinkafa.

“Abin takaici, yawancin ɗalibanmu mata sun sami raunuka da dama, yayin da wasu suka sha wuya saboda yawan jama’a a wurin da aka raba kayan abinci.

“A yanzu haka, ina Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Keffi, inda muka kawo wasu daga cikin ɗalibanmu domin ba su kulawar gaggawa.

“Har ila yau, a matsayina na shugaban ƙungiyar NASA na ƙasa, na samu rahoto a hukumance cewa ɗalibi ɗaya ya mutu sakamakon wannan mummunan lamari.

Mataimakain gwamnan jihar ta Nassarawa, Emmanuel Akadeh wanda ya je jami’ar domin jajantawa dangane da faruwar al’amarin ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici kuma “za mu kafa kwamitin da zai binciko hakikanin abin da ya faru.”