✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙiba ta kashe birin da ake ciyar da shi kayan daɗi

Masu Godzilla sun ce sun ɗauko shi yana ƙarami bayan da mota ta kashe iyayensa kuma aka yi watsi da shi.

Wani biri mai suna Godzilla ya yi fama da jinya da masu wucewa ke bai wa kyaututtuka a birnin Bangkok na ƙasar Thailand, bayan ya kamu da cututtuka masu yawa da suka shafi ƙiba yana ɗan shekara shida.

A ranar 6 ga Mayu, Godzilla ya yi numfashinsa na ƙarshe a Asibitin Crystal Pet da ke Bangkok yayin da ubangidansa ya riƙe hannunsa.

Sai dai mutumin da iyalansa suna fuskantar suka daga jama’a kan zargin kashe birin saboda irin kyautatawar da suke yi wa birin tare da shagaltuwa da shaye¬shayen kayan zaƙi da sauransu tare da mayar da shi abin sha’awa a rumfar kasuwarsu.

Masu yawon buɗe-ido masu wucewa sanye da rigar shan iska kan ciyar da shi duk wani nau’in abinci mai kyau, wanda hakan ya kai shi yin nauyi sama da kilo 19, inda ya ninka nauyin matsakaicin biri nau’insa.

Abin baƙin ciki, yanayinsa bai taɓa samun sauyi ba bayan kamuwarsa da cutar, inda wasu cututtuka masu alaƙa da ƙiba suka yi sanadin kashe shi.

Birin na iya rayuwa har shekara 37, amma Godzilla ya mutu yana da shekara 6 kacal. Sa’an nan, ya yi fama da ciwon sukari da ciwon dajin maƙoshi, saboda cin abinci mai daɗi da abubuwan sha.

Jama’a na son kallonsa yana cin abinci kuma suna kawo masa abinci iri-iri a rumfar kasuwar ubangidansa. Wannan ya sa ake cewa sun kashe shi da kayan daɗi.

Masu Godzilla sun ce sun ɗauko shi yana ƙarami bayan da mota ta kashe iyayensa kuma aka yi watsi da shi.

Duk da sanin cewa dokar ƙasar ta hana ajiye biri, masu shi sun tsare Godzilla ɗaure a rumfarsu ta kasuwar nama inda a ƙarshe ya zama abin sha’awa ga masu yawon buɗe-ido.

Bayan da hukumomi suka ɗauke shi shekara uku da suka gabata, Godzilla ya fuskanci ‘Tsananin kitse’ a wata cibiyar namun daji da ke Lardin Chachoengsao inda ake ba shi abinci mai inganci.

Da farko an hana mamallakansa ganinsa, amma daga ƙarshe an ba su izinin yin mu’amala da shi kuma sun kasance a gefensa har a lokacinsa na ƙarshe.

“Mun yi baƙin cikin mutuwarsa. Ya kasance kamar danginmu. Mun ceto shi lokacin da aka watsar da shi kuma muka kyautata masa,” in ji tsohon ubangidansa.

Ya ƙara da cewa, “Bai kamata a ɗauke shi daga gidansa ba saboda yana son cin abincin da muke ba shi.”