Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan ƙasar Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota.
Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain.
- ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara
- NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta
Jota ya rasu yana da shekara 28 a duniha.
Hatsarin ya faru ne a hanyar A-52, kusa da garin Palacios de Sanabria.
Jota yana cikin motar tare da ɗan uwansa, André Silva, wanda shi ma ya rasu.
Silva ɗan wasa ne da ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon kafa ta Penafiel a ƙasar Portugal.
Rahotanni sun ce motar ta ƙwace ne tare da barin hanya sannan kuma ta kama da wuta.
Jami’an agaji da ma’aikatan kashe gobara daga Rionegro del Puente sun isa wajen cikin gaggawa, amma ba su iya ceto rayuwar mutanen da ke cikin motar ba.
Hukumomi har yanzu suna bincike don gano musabbabin aukuwar hatsarin.