Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun baƙunci lahira, bayan cin ɗan wake a garin Karkari da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
Waɗanda suka rasun sun haɗa da Alhakatu Abdulkarim da ‘ya’yanta biyar da suka haɗa da Bashir Abdulkarim da Firdausi Abdulkarim da Hafsat Abdulkarim da Usman Abdulkarim da Jamilu Abdulkarim.
- An kama wata mata da makamai a cikin buhun garin kwaki
- An ɗaure mutum 1000 saboda zanga-zangar yunwa — Amnesty
Wani mazaunin garin, mai suna Garba Muhammad, ya shaida wa Aminiya cewa yanayin da ake ciki na fatara da yunwa ya sanya marigayiyar yin amfani da wani ajiyayyen garin rogo, wajen dafa ɗan waken da suka ci tare da iyalanta.
Sai dai daga cin ɗan waken ne, ciwon ciki ya murɗe su inda daga bisani suka rasu.
“Kin san halin da ake ciki na rashin abinci, hakan ya sa marigayiyar wacce uwar marayu biyar ne, yin amfani da wani ajiyayayyen rogo ta haɗa ɗan wake da shi.
“To Allah cikin ikonsa bayan sun ci da8n waken ne, wannan Iftila’i ya saukar musu inda suka mutu gaba ɗaya.”
Mutumin ya bayyana cewar suna zargin tsaka da shiga cikin garin rogon wanda ya daɗe a ajiye.
Kakakin rundunar jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faduwar lamarin.
Ya ce bayan lamarin ya faru an garzaya da mutanen Babban Asibitin Gwarzo, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Kiyawa, ya ce tuni rundunar ta fara bincike kan lamarin.