Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar ƙasurgumin ɗan daban nan da ya addabi jihar, Abba Burakita.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
- ’Yan bindiga sun kashe dan sanda da dan banga a Sakkwato
- An kama hedimasta kan sayar da kujerun makaranta a Kano
Burakita, dai ya yi ƙaurin suna wajen harkar daba, fashi da makami, ƙwace, sara-suka da sauran miyagun laifuka.
Kiyawa ya ce “ɗan daban da muka kama, kuma dama muna nemansa a bisa zargin laifukan fashi da makami da jagorantar harkar daba; Abba Burakita, ya rasu,” in ji shi.
Idan ba a manta ba Burakita yana daga cikin ’yan daban da suka hana unguwar Ɗorayi zaman lafiya.
Mazauna unguwar sun jima suna kai kokensu ga hukumomi domin kawo ƙarshen ayyukan ‘yan daba.
Wannan dalili ne ya sanya, Gwamnatin Kano amincewa domin gina sabon ofishin ’yan sanda a unguwar domin kawo ƙarshen ayyukan daba.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta jima tana nemansa ruwa a jallo, amma bai zo hannunta ba sai a ƙarshen makon da wuce.
Rahotanni sun bayyana cewar an kama ne lokacin da shi da wasu yaransa ke ƙwacen waya a kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar.
An ce ya samu rauni sakamakon arangama da ya yi jami’an tsaro, wanda daga bisani likitoci a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad suka tabbatar da mutuwarsa.