✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙara Farashin Mai: Tinubu ya yaudare mu —NLC

NLC ta ce gwamnatin Tinubu ta ƙware wajen yin kama-karya.

Shugabancin Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), ya zargi Shugaba Bola Tinubu da yaudararsu, ta hanyar karya alƙawarin da suka yi tare da ƙara farashin man fetur.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana rashin jin daɗinsa a ranar Talata game da ruɗanin da ke tattare da farashin man fetur, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “abin damuwa.”

Ajaero, ya bayyana yadda Tinubu ya bai wa NLC da TUC zaɓin; su amince da mafi ƙarancin albashin Naira 250,000 tare da ƙara farashin mai ko kuma su aminta Naira 70,000 tare da an ƙara farashin man ba.

NLC, ta zaɓi ƙaramin albashin don kaucewa ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin matsin rayuwa.

Sai dai Ajaero ya soki gwamnatin saboda ƙarin farashin mai da aka yi maimakon barinsa yadda yake.

Ya bayyana cewar wannan ƙarin zai ƙara jefa ‘yan Najeriya da kasuwanci cikin tsaka mai wuya.

Ya ce, “Mun tuna lokacin da Shugaban ƙasa ya ba mu zaɓi mai wuya tsakanin mafi ƙarancin albashi na Naira 250,000 tare da ƙara farashin man fetur zuwa Naira 1,500 ko Naira 2,000 kan kowace lita, ko kuma mu aminta da Naira 70,000. Mun zaɓi ƙaramin albashin don gujewa ƙara azabtar da ‘yan Najeriya.

“Amma yanzu, ba a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba, gashi muna fuskantar yanayin da ba mu fahimta ba. Wannan abin damuwa ne.

“Muna gargaɗin gwamnati cewa hanyar da suka ɗauka wajen kawo ƙarshen tallafin man fetur ba daidai ba ne kuma ba za ta ɗore ba, amma sun yi watsi da gargaɗinmu, suna cewa ba mu fahimci yanayin da tattalin arziƙi ke ciki ba.

“Wannan yaudara daidai ta ke halayyar wannan gwamnati. Mun tuna alƙawuran da shugabannin Majalisar Ƙasa suka yi mana kan ƙarin kuɗin wutar lantarki na kashi 250, sun tabbatar mana da cewa an magance matsalar kuma babu buƙatar mu fuskanci Ministan Wutar Lantarki.

“Amma maimakon dawo da ainahin kuɗin wutar, sai gwamnati ta ƙara kuɗin wutar lantarki, wanda ya jefa ‘yan Najeriya da kasuwanci cikin hatsari.

“Manufofin gwamnatin nan masu tsanani sai jefa ‘yan Najeriya cikin matsanancin talauci suke yi wanda ya haifar da zanga-zangar matsin rayuwa.”