Akan samu yara masu shekara 10 zuwa 13 su haddace Alkur’ani Mai girma, inda a wasu lokuta ma akan samu wadanda suke haddace shi tun ba su wuce shekara bakwai ba.
Sai dai abin mamakin shi ne yadda wata yarinya ta rubuta cikakken Alkur’ani Mai girma da ka a daidai lokacin da take da shekara 13.
- Sadakin Naira dubu 50 tozarta aure ne —Sheikh Kaura
- ’Yan Najeriya 56 sun mutu sun bar dukiya babu magada a Birtaniya
Yarinyar mai suna Zuwaira Ahmad daliba ce a Makarantar Madrasatu Tahfizil Kur’an Waddirasatil Islamiyya da ke kauyen Kagara a Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina inda aka ce ta rubuta cikakken Kur’ani Mai girma a cikin wata biyu.
Malama Zuwaira ta fara rubutu na biyu a ranar Litinin da ta wuce, inda take fatar kammalawa cikin kankanin lokaci.
“Abin da ya shagaltar da ni da kuma natsuwa gaba daya a halin yanzu shi ne karatu da rubuta Alkur’ani Mai girma kuma babban burina shi ne in ga cewa na samu ilimi mai yawa kuma mutane da yawa su amfana da abin da na samu,” inji ta.
An shigar da Zuwaira makarantar Islamiyya a kauyensu Kagara, tana da shekara bakwai, inji mahaifinta, Malam Ahmad Ibrahim Kagara, inda ta haddace Alkur’ani a cikin shekara shida.
“Yau tana da shekara 13 da wata hudu, mun shigar da ita tana da shekara bakwai da wata uku, duk abin da ta samu ta fuskar hadda da rubuta Alkur’ani Mai girma tana makaranta daya ba ta taba zuwa wata makarantar ba.
“Muna matukar godiya ga Allah Madaukakin Sarki yayin da ta rubuta Alkur’ani a cikin wata biyu da ’yan kwanaki. Da ta yi sauri fiye da haka idan ban da mukan nemi ta huta sau daya,” inji shi.
Malam Ahmad Ibrahim, wanda ya bayyana matukar farin cikinsa kan abin da ya kira baiwar Allah ga iyalansa, ya yi kira ga iyaye su kasance masu rikon amana ga ’ya’yansu.
“Hakkinmu ne a matsayinmu na iyaye, mu kula da iyalanmu, kula da lafiyarsu da iliminsu da tarbiyyarsu.
“Idan muka kasa yin haka, muka bar ’ya’yanmu su rike kansu, to, ba mu sauke nauyin da Allah Ya dora mana ba.
“Kuma da haka muke bude kofofin rashin da’a a cikin al’ummarmu. Koda yake ina zaune a kauye, ba na kyale ’ya’yana su je gona ko su yi bara a titi ko wani abu daban.
“Ina kokari a cikin karancin albarkatuna in kula da su. In har muka samu damar gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata, gidajenmu za su yi kyau, al’ummominmu za su yi kyau kuma za mu samu al’umma mai wadata,” inji shi.
Mahaifin yarinyar ya kara da cewa, yana da wasu ’ya’ya biyu Abubakar da Siddika, wadanda ya ce sun nuna hazaka irin ta babbar yayarsu Zuwaira.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatoci da masu hannu da shuni su zakulo tare da tallafa wa yara masu hazaka.
Da take zantawa da wakilinmu Malama Zuwaira, ta ce idan ba don Kur’ani Mai girma ya kawar da alfahari ba, tana iya cewa ta samu sauki sosai Juma’a, 16 ga Satumba, 2022 wajen hadda tare da rubuta cikakkensa.
Ta danganta nasarar da ta samu wajen karatu da rubuta Alkur’ani Mai girma n ga tallafin da iyayenta suka ba ta, inda ta ce duk da karancin albarkatun da suke da ita, suna biya mata bukatun yau da kullum, kuma ga jajircewar malaminta Malam Hassan Lawal.
“Ba na shiga cikin wani shawagi ko wani abu da zai raba hankalina. Ina jin dadin tallafin dabi’a da na kudi daga iyayena, musamman mahaifina wanda ya sayi duk abin da nake bukata daga aikina na rubuta Kur’anin.
“Don haka ina kira ga iyaye su tallafa wa ’ya’yansu domin su samu damar mayar da hankali a kan karatunsu na boko ko na addini ko duka biyun,” inji ta.
Da aka tambaye ta ko tana karatun boko? Malama Zuwaira ta ce, a’a, amma wasu malamai kan ziyarci makarantarsu ta Islamiyya don koyar da su ilimin boko da ilimin lissafi, kamar hadaddiyar Makarantar Tsangaya ta tsara.
Sai dai a bayyane yake cewa Malama Zuwaira ba ta da jagora don sanin abin da za ta karanta a makarantar boko ko abin da take son zama a nan gaba.
“Zan so in ci gaba da karatun kasashen Yamma kuma ba ni da wani buri na abin da nake so in karanta ko zama a nan gaba, zan yarda da duk abin da iyayena suka zaba mini,” inji Zuwaira.
Yarinya ce ta musamman, za ta iya yin fice a duniya idan aka tallafa mata —Malami
Shugaban Makarantar Madrasatu Tahfizil Kur’an Waddirasatil Islamiyya, Malam Sani Kagara, ya ce Zuwaira ta yi fice domin babu wata daliba da ta nuna hazaka a makarantar kamarta.
“Ita kadai ce daga cikin tsararrakinta da ta nuna irin wadannan halaye na musamman. Wasu kuma sun rubuta cikakke Alkur’ani amma bayan sun girma, amma Zuwaira nakan yi mamaki duk lokacin da take karatun Kur’ani da kyau da kyau,” inji shi.
Ya bayyana ta a matsayin yarinya mai biyayya da kyakkyawan hali da ke mai da hankali kan abin da take koya kuma ta sadaukar da lokacinta wajen rubuta Alkur’ani Mai girma.
Ya ce an kafa makarantar ne domin tarbiyya da ingantaccen ilimin addinin Musulmi a tsakanin matasa kuma suna karatu daga karfe 7:00 na safe zuwa 6:00 na yamma tare da hutun cin abinci da Sallah a tsakani.
A cewarsa, yarinyar ta haddace Alkur’ani ne a cikin shekara hudu, kuma ya danganta nasarar da suka samu ga goyon bayan iyayenta da jajircewar malamanta a makarantar.
Ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba ta goyon bayan da ya dace don ta ci gaba da karatunta na boko inda ya ce a yanzu tana makarantar firamare a yankin.
Ya ce idan yarinyar za ta samu tallafi wajen karanta Tajwidin Alkur’ani, za ta iya shiga gasar Musabaka a matakan kananan hukumomi da jihohi, da na duniya.
Da yake jawabi a wajen bikin karrama yarinyar a ranar Asabar das ta gabata, Hakimin Mahuta kuma Danejin Katsina, Alhaji Bello Abdulkadir, ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba.
Ya ce wannan babbar nasara ce ga al’umma da jihar baki daya, musamman a bangaren ilmin addinin Musulunci.
Danejin Katsina ya yaba wa iyaye da malamai da sauran shugabannin al’umma a yankin kan yadda suke kula da tarbiyyar ’ya’yansu yadda ya kamata, yana mai kira gare su kan su ci gaba da yin haka.
Ya tabbatar da himmar masu rike da sarautu ta ci gaba da bayar da goyon baya ga dukkan al’amuran da suka shafi addini domin ci gaban yankin baki daya.
A jawabin Shugaban Karamar Hukumar Kafur, Alhaji Garba Abdullahi Kanya, ya yaba da kwazon yarinyar tare da ba da tabbacin tallafa wa karatunta a matakin sakandare.