Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya bayyana kudirin sake gina wasu kauyuka uku domin sake tsugunar da ’yan gudun hijirar da mayakan Boko Haram suka raba da muhallansu a Jihar a shekarun baya.
A shekarun baya ne dai rikicin Boko Haram da ya dabaibaye Jihar da sauran makwabtanta da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya aka samu fiye da mutum miliyan biyu da muhallansu a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda wasunsu ke zaune a makwabtan kasashen kamaru da Chadi da Nijar.
- Matana da ’ya’yana ba za su shiga gwamnatina ba — Abba Gida-Gida
- NDLEA ta kama wasu mata 2 da tabar wiwi a Katsina
Kamar yadda gwamnan ya ambata a cikin wani sako a shafinsa na Twitter, ya ce tun shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka raba mutanen da muhallansu na asali suka zama ’yan gudun Hijira.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da kwamitin mayar da ’yan gudun hijirar da ke kasashen waje a Abuja, karkashin shugaban Kwamitin Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osunbanjo.
Gwamna Zulum dai shi ne Mataimakin Shugaban kwamitin na Shugaban Kasa na mayar da ’yan gudun hijirar kasar da ke zaune a kasashen waje, tare da sauya tunanin mutanen da Boko Haram ta sako su.
A cewar Gwamna Zulum, Shugaba Buhari ya amince da bai wa kwamitin nasu kimanin Naira biliyan 15, yayin da gwamnatin Jihar ke shirin sake gina kauyuka uku don tsugunar da ’yan gudun hijirar don su ci gaba da rayuwa da ’yan uwansu.