Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba da umarnin gina gidaje 500 a garin Nguro Soye, da ke Karamar Hukumar Bama domin tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.
Zulum ya kuma sa gyara wasu gidaje 1,000 a garin da aka lalata a hare-haren kungiyar.
- Abin da ya sa aka umarci jihohi su dakatar da yin rigakafin COVID-19
- Dalilai uku na sauke Sufeto Janar Mohammed Adamu
- An sake kai wa ofishin ’yan sanda hari a Imo
Ya ba da umarnin gudanar da ayyukan ne a lokacin da ya ziyarci Bama a ranar Talata.
A lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Shehun Bama, Shehu Umar Ibn Kyari Ibrahim El-kenemi, gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da ganin karin yara a jihar na samun halartar makarantu.
Ya kuma amince da bukatar da Shehun Bama ya gabatar mas na kara tallafa wa manoma gabanin faduwar damina da ke kara karatowa a Jihar.