Gwamnan Borno, Babagana Zulum Talata, ya ziyarci sansanin ’yan gudun hijira a Baga Sola, mai iyaka da kasar Chadi domin ganawa da ’yan asalin jiharsa.
Ziyarar ta zo ne kwanaki biyu bayan mahara sun kashe mutum 50 daga cikin ’yan Karamar Hukumar Abadam ta jihar da ke gudun hijira a garin Tumuk na Jamhuriyar Nijar.
- Boko Haram ta bindige ’yan gudun hijirar Najeriya 50 a Nijar
- Boko Haram ce ta yi garkuwa da daliban Kankara —Shekau
- ’Yan Boko Haram sun kai hari wani gari a Borno, sun yi kiran Sallah
- Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 27 a Nijar
Sanarwa da hadimin gwamnan kan watsa labarai, Isa Gusau, ya fitar ta ce Zulum ya gana da ’yan gudun hijirar, inda ya musu alkawarin gudunmawa da tallafi.
Isa Gusau ya ce gwamnan ya jagoranci rabon tsabar kudi Naira miliyan 50 ga iyalai 5,000, wanda kowannensu ya samu 10,000.
Zulum wanda ya samu rakiyar Jakadan Najeriya a Chadi da kuma Jakadan Chadi a Najeriya, ya ce gwamnatinsa na kokarin hadin gwiwa tare da cibiyoyin tarayya da UNHCR domin dawo da ’yan gudun hijirar Borno.
Daga nan gwamnan, ya zarce zuwa N’Djamena, babban birnin Jamhuriyar Chadi, inda zai gana da wasu ‘yan gudun hijira daga Borno, a ranar Laraba.
Gwamnan ya tafi tare da dan majalisar tarayya ami wakiltar Kukawa, Haruna Kukawa, kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Sugun Mai Mele, Mashawarci na Musamman kan harkar Gidaje da Makamashi, Zanna Jabu da manajan Kamfanin Plastics Industries Abatcha Jarawa.