✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya ziyarci iyayen wanda Boko Haram suka sace a Chibok

Gwamnan ya jajanta wa iyalan wanda aka kashe da wanda aka sace wa 'yan uwa.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ziyarci garin Chibok inda ya gana iyalan wadanda mayakan Boko Haram suka sace a kauyukan Kawtakare, Korohima da Pemi.

Gwamnan ya kuma gana da iyalan wadanda aka sace mutum 24, yayin harin da Boko Haram ta kai yankin.

Mayakan na Boko Haram dai sun kai farmaki kauyen Korohuma a ranar 30 ga watan Disamba 2021, sai kauyen Pemi a ranar 14 ga Janairun 2022 da kuma Kautakare a ranar 21 ga watan Janairun 2022.

Gwamnan ya ce “Mun zo don mu jajanta wa iyaye da ’yan uwan wanda aka sace da kuma mutum hudu da Boko Haram ta kashe. Tabbas ranmu ya sosu, kuma muna fatan kar hakan ta sake faruwa a gaba.”

Kazalika, Gwamnan ya kuma gana da shugabannin tsaron yankin inda ya tattauna muhimman abubuwan da suka shafi tsaron yankin.

A baya-bayan nan, yankuna hudu na Jihar; Biu, Askira, Chibok da Damboa, sun sha fama da hare-hare daga mayakan Boko Haram da na ISWAP.

Da ya ke wa Gwamnan jawabi kan yadda harin ya faru, shugaban karamar hukumar Chibok, Umar Ibrahim ya ce an sace kimanin mutum 24 yayin da kuma aka kashe mutum hudu.

Sannan shugaban Karamar Hukumar ya kara da cewar, mayakan sun kone gine-gine 110 wanda suka hadar da gidaje 73 da shaguna 33, coci guda hudu, motoci takwas da kuma babura uku.

Zulum ya bada umarnin yin bincike tare da gano adadin asarar da mutanen yankin suka yi a sakamakon harin.

Gwamnan ya kuma jinjina wa Shugaban Karamar Hukumar ta Chibok kan irin kokarin da ya ke wajen jagorantar al’ummar yankin.