✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya ziyarci Chadi kan dawo da ’yan gudun hijira

Ya ba wa masu gudun hijirara tabbacin dawowarsu gida Najeriya

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya ziyarci Shugaban Kasar Chadi, Idris Deby, domin tattaunawa kan dawowar ’yan Jihar Borno da ke gudun hijira a kasar ta Chadi.

Akasarin ’yan gudun hijirar sun tsere ne daga Jihar Borno tun daga shekarar 2014 bayan hare-haren kungiyar Boko Haram sun tsananta.

“Mun tattauna yadda za mu maido da mutanenmu gida Najeriya. Mun zo ne domin abubuwa uku: ganawa da mutanenmu, yin godiya ga Gwamnatin Chadi da kuma da kuma karfafa hadin gwiwa a kokarin maido da wadanda suke sha’awar komawa Borno”, inji Zulum.

A ziyarar Gwamnan tare da Jakadan Najeriya a Chadi, Zannah Umar Bukar Kolo, ya gana da ’yan gudun hijirar, inda ya ba su tabbacin samun tallafi da kuma shirin maido wa su zuwa garuruwansu.

“Mutanenmu na zaune lafiya; Gwamnatin Chadi na kula da su. Na zo ne domin in yi godiya ga Shugaban Kasa saboda tagomashin da ya yi wa jama’armu da ke Chadi”, inji shi.

A watan Janairu, Gwamna Zulum ya ziyarci kasar Chadi inda ya gana da kwamnadojijn Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa ta MNJTF mai yaki ta ta’addanci.

Ziyarar tashi zuwa Chadi na zuwa ne ’yan kwanaki bayan mayakan Boko Haram sun kai hari a kan ’yan jihar da ke gudun hijira a Jamhuriyar Nijar inda suka kashe mutum 50.