Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yanka wa ’yan sa-kai da ma’aikatan tsaftar muhalli a Jihar albashi, tare da kyautar kudi da kuma buhun shinkafa ga kowanensu.
Zulum ya sanar da hakan ne a matsayin wani bangare na kara wa ’yan agajin da ma’aikatan tsaftar muhallain jihar kwarin gwiwa.
Ya ce alherin kudi da aka ba su godiya ce gami da yabawa kan irin kokarinsu wajen yaki da ’yan ta’adda a jihar.
“’Yan sa-kanmu, kun jima kuna aiki tukuru don ceto jihar Borno. Duk da cewa kuna da yawa, amma ko nawa aka ba ku ba a yi asara, ba duba da yadda kuke sadaukar da rayukanku. A madadin daukacin al’ummar Jihar Borno muna godiya a gare ku,” a cewar Zulum.
Kazalika, yayin da ya ke jawabi ga masu aikin tsaftar muhallin jihar, ya ce, “Da yawa daga cikinku kuna tashi karfe 6 na safe ku share tituna. Yawancinku da su ake aikin gyaran wasu tituna. Muna godiya tare da yaba muku kan wannan kokari da kuke yi.”
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafawa tare sa kyautata wa jama’ar da ke kokarin kawo ci gaba a jihar.