Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya raba tallafi ga manoma 1,200 da suka koma gidajensu a garin Damasak a Karamar Hukumar Mobbar.
Mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
- Turawa sun fi Larabawa taimaka wa Jihar Borno —Zulum
- ’Yan gudun hijira 800,000 ne a sansanoni ke bukatar tallafin abinci – Zulum
Gusau, ya ce a wannan yunkuri ne na farfado da harkar noma a Jihar, manoman sun samu tallafin taki, iri, sinadarin shuka, da kuma kudi 5,000 ga kowanne daga cikin manoman 1,200.
Mazauna garin, karkashin jagorancin Sanata Abubakar Kyari, sun yi alkawarin kara bunkasa harkar noma, don cika burin gwamnatin jihar.
Zulum ya ce tallafa wa manoman, ita ce hanya kadai da za a iya farfado da kalacewar harkar noma a Jihar.