Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya samun tikitin sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar a jam’iyyar APC ba tare da abokin hamayya ba.
Gwamnan ya sake samun tikitin ne bayan da daliget din jam’iyyar suka zabe shi a ranar Laraba a Maiduguri.
- Gwamnan Anambra ya ba mijin da aka kashe wa mata da ’ya’ya N500,000
- Muhammad Abacha ya zama dan takarar Gwamnan PDP a Kano
Zulum ya gode musu tare da jinjina musu kan sake ba shi damar yin takarar Gwamnan Jihar a babban zaben 2023 da ke zuwa.
Sai dai Gwamnan ya ki amincewa da tayin takarar Mataimakin Shugaban Kasa da wasu jiga-jigan ’yan siyasar kasar nan suka masa.
Zulum ya ce, “Ina so na fara da ba da hakuri ga wasu manyan na kusa da masu neman takarar Shugaban Kasa da suka min tayin takarar Mataimakin Shugaban Kasa.
“Na yi tunani sosai kan yadda kujerar Mataimakin Shugaban Kasar ke tattare da alfarma. Yadda Gwamnoni ke halartar taruka da kuma yadda ake girmama su.
“Sai dai na tambayi kaina idan na karbi tayin takarar, wa zai ci gaba da ayyukan alheri ga mutanen Jihar Borno?
“Na fahimci zama Mataimakin Shugaban ni kadai zai amfanar, don haka ya sa na ki karba, na gwammace na sake zama Gwamnan Borno don ciyar da ita gaba.
“Don haka ina godiya ga wadanda suka yi tunanin ba ni damar yin takarar, amma na fi sha’awar ci gaba da yi wa Jihar Borno aiki, a matsayina na dan asalin Jihar,” cewar Gwamna Zulum.