✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya raba wa ’yan gudun hijira sabbin takardun kudi a Borno

Ya raba musu tallafin ne bayan sun koma gidajensu bayan shafe wata bakwai

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Rann, hedkwatar Karamar Hukumar Kala-Balge ta Jihar inda ya raba sabbin takardun kudi ga sama da ’ya gudun hijira 12,000 da suka koma gidajensu.

Gwamnan dai ya sauka garin ne ta jirgin sama mai saukar ungulu, inda ya sa ido a kan yadda aka raba sabbin takardun kudin.

A cewar Gwamnan, an dauki matakin ne domin bai wa ’yan gudun hijirar da ke zaune a yankin damar siyan kayan abinci don ciyar da kansu da iyalansu.

Idan dai za a iya tunawa, tun lokacin da aka yi tashe-tashen hankula, ambaliyar ruwa ta raba al’ummar yankin da muhallai da gonakinsu, inda tilasta musu yin kaura tare da zama da karancin abinci daga kauyukan da ke kan iyaka da Najeriya da Jamhuriyar Kamaru.

Hakan ya sa ba za a iya isa garin Rann ta hanya daga garin Dikwa ba sai ta garuruwan kan iyaka ko yankunan da ke kusa da Jamhuriyar Kamaru.

Da yake zantawa da manema labarai lokacin raba tallafin, Gwamna Zulum ya ce, “Abin takaici, an raba wannan al’umma daga sauran sassan Najeriya tsawon watanni bakwai da suka wuce, ba su da ko daya daga cikin kayayyakin aiki, saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da karancin hanyoyin shiga yankin.

“Muna nan Rann ne don samar da wasu kayan agaji ga kusan magidanta 12,000 da ke zaune a nan,” in ji Zulum.

Sai dai kuma kafin Gwamnan ya kai ziyara, al’ummar garin Rann sun koka kan yadda ’yan kasuwa da sauran kananan ’yan kasuwa ba sa karbar tsoffin takardun Naira a hannunsu saboda sanarwar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ta daina amfani da su daga ranar 31 ga watan Janairun 2023.

Yayin ziyarar kuma, Gwamna Zulum ya duba ayyukan da gwamnatin Jihar ke ci gaba da yi wadanda suka hada da babban asibitin garin na Rann wanda an riga an kammala shi.

Ya kuma ziyarci sabuwar sakatariyar Karamar Hukumar Wanda aikin ya kai sama da kasO 70 cikin 100 da kuma babban masallacin garin da aikin sa shi ma ya yi kusan kammaluwa da kusan kaso 70, yayin da shugaban riko na Karamar Hukumar, Zannah Jabu ya jagoranci Gwamna wajen duba ayyukan.

Gwamna Zulum ya yi tattaki zuwa Rann ne tare da dan takarar kujerar Sanatan Borno ta t]Tsakiya na jam’iyyar APC da wasu jiga-jigan gwamnatinsa.