Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba kuɗi Naira miliyan 150 ga mata 15,000 tare da kayan abinci a ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar.
Gwamnan, ya kuma raba buhun masara wanda Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihohi ga magidanta 10,000, domin rage wahalhalu da matsin rayuwa.
- Ma’aikata ku tsaida harkokinku idan aka kama Ajaero – NLC
- Hisbah ta kama kwalaben barasa 24,000 a Kano
Zulum, ya ce an kuma miƙa makamancin kayan ga mazauna ƙananan hukumomin Gwoza da Nganzai.
“Wannan kayan abinci shi ne kashin ƙarshe wanda Gwamnatin Tarayya ta bai wa jihar, wanda idan za a tuna mun raba irin wannan kayan abinci a Gwoza da Nganzai watannin da suka gabata,” in ji Zulum.
Gwamnan, ya kuma ce kowace mace daga cikin mata 15,000 za su samu Naira 10,000 daga ƙananan bankuna a matsayin tallafi.
Don haka ya nemi dukannin waɗanda suka amfana da su taya jihar da ma ƙasa baki ɗaya da addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya mai ɗorewa.