✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya raba tallafin rage radadi ga iyalai 2,000 a Borno

Mun raba buhun shinkafa 3,000 daga cikin kason da muka karba daga Shugaba Tinubu.

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya jagoranci shirin rage radadi da ya kunshi rabon tallafin abinci ga iyalai 2,000 a mazabar Mafoni da ke birnin Maiduguri.

Wata sanarwa da Mallam Isa Gusau mai magana da yawun gwamnan ya fitar ta ce manufar rabon abincin ita ce rage radadin cire tallafin man fetur, kuma yayin rabon an bai wa kowanne gida buhun shinkafa da wake biyu.

Zulum ya bayyana cewa an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga mazaba 27 daga fadin Maiduguri da kuma mazaba 12 daga Karamar Hukumar Jere.

Sanarwar ta ce rabon abinci wanda ya kunshi buhun shinkafa 54,000 da buhunnan wake 54,000, an bayar ne ga magidantan da suka fi bukata a cikin kananan hukumomin jihar biyu, a cewar gwamnatin.

Ta kara da cewa gwamnatin Zulum ta tashi haikan wajen neman dabarun da za su rage illar da hauhawar farashin man fetur ta haifar a kan talakawa, ta hanyar tabbatar da ganin abinci da sauran muhimman ayyuka ga masu tsananin bukata.

Da yake jawabi a wurin raba abincin, Gwamna Zulum ya ce buhunnan shinkafar wani bangare ne na shinkafa buhu 3,000 da gwamnatin Borno ta karba daga Shugaba Bola Tinubu.