✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai magana da yawun Gwamna Zulum, Isa Gusau ya riga mu gidan gaskiya 

Mun rasa Gusau bayan ya yi kusan kwana uku a sume saboda tsananin jinya da ya yi fama da ita.

Allah Ya yi wa mai magana da yawun Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum rasuwa.

Malam Isa Gusau ya rasu ne a wani asibiti a ƙasar Indiya a jiya Alhamis, inda ya yi doguwar jinya kamar yadda wakilinmu ya ruwaito.

Malam Isa Gusau, ya riƙe mukamin mai magana da yawun tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, wanda a yanzu shi ne Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya.

Bayanai sun ce Malam Isa Gusau ya kwashe sama da wata guda yana jinya a wani asibiti a Indiya.

Majiyar ta ce: “mun rasa Gusau da sanyin safiyar ranar Alhamis inda ya yi kusan kwana uku a sume kafin rasuwar sa.

“Duk mun yi masa addu’ar samun lafiya, amma Allah bai yarda kuma Ya karbi abinSa kasancewar Ya fi mu sonsa.”

Makusanta da ke ci gaba da alhini sun bayyana marigayi Isa Gusau a matsayin mutumin kirki da taka-tsan-tsan kan harkokin rayuwa wajen ganin ya sauke nauyin duk wanda ya rataya a wuyansa.

Har yanzu dai ba a bayyana lokacin da za a dawo da gawarsa gida Najeriya ba domin yi masa jana’iza.