✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An shiga rudani a majalisa yayin tantance Festus Keyamo

Majalisar ta ce Keyamo ba ya amsa goron gayyatarta a lokacin da yake minista a Gwamnatin Buhari.

An shiga rudani a Majalisar Dattawa yayin tantace Festus Keyamo a matsayin daya daga cikin wadanda Shugaba Bola Tinubu zai bai wa mukamin minista.

A halin yanzu dai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya isa Fadar Shugaban Kasa bayan zazzafar muhawarar da ta barke a zauren majalisar yayin tantance babban lauyan daga Jihar Delta.

Gabanin haka dai, majalisar ta soma shiga zaman sirri saboda sabanin da ya rincabe tsakanin sanatoci a kan tantance Mista Keyamo.

Sanata Darlington Nwokocha ne ya fara gabatar da kudirin dakatar da tantance Mista Keyamo a gaban majalisa, inda ya nemi a dakatar da shi har sai lokacin da ya amince da cewa majalisa na da damar bincikar ayyukan ministoci.

Hakan ya faru ne sakamakon tirjiyar da ya nuna a lokacin da yake minista a baya, inda ya ki amsa gayyatar majalisa.

Kudirin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, hakan ya sa daga karshe majalisar ta yanke shawarar shiga zaman sirri kan lamarin.

Festus Keyamo shi ne ministan gwamnatin Buhari da ya sake shiga cikin jerin sunayen wadanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nada a matsayin minista.