Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba kudade kimanin Naira miliyan 275 tare da buhunan hatsi, da tufafi ga magidanta kimanin 90,000 da ke gudun hijira a Monguno da ke Jihar.
A tsawon shekaru ukun da ya yi a kan mulki, Gwamnan dai ya rika raba irin wannan tallafi a wani bangare na kokarin kara wa al’ummar da hare-haren Boko Haram ya shafa karfin gwiwa.
- ’Yan sanda sun kama matashi da kullin Tabar Wiwi 250 a Kano
- Galadiman Jama’a ya rasu yana da shekara 73
Ana ganin tallafin ma taka muhimmiyar rawa wajen dakile yunkurin Boko Haram na daukar ’yan leken asiri daga talakawa da marasa galihu, ta hanyar bai wa wasu mazauna yankin kudin da bai wuce N5,000 ba, a matsayin tallafin kudi.
Gwamna dai ya yi tattaki ne tare da babban mai shigar da kara na Majalisar Wakilai, Barista Mohammed Tahir Monguno inda ya kwana a garin Mafa, kuma ya isa Monguno da safiyar Juma’a domin fara ayyukan jin kai.
Garin na Monguno ya karbi bakuncin ’yan gudun hijirar da suka fito daga Kananan Hukumomi kusan biyar da ke gefen tafkin Chadi, da kuma na Jamhuriyar Nijar bayan sun tsere daga hare-haren Boko Haram a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014.
Gwamna Zulum ya kuma sa ido kan rabon kudaden da sauran kayayyaki da aka tanadar musu yadda aka ba da N5,000 ga mata 55,000, wanda adadin ya kai Naira miliyan 275.
Bayan ganawarsa da mata a tsawon yini, Zulum ya kara sa ido a tsakar dare domin kaiwa ga shugabanni da kuma magidanta 35,000 da suka yi layi cikin daren yadda aka ba kowanne daga cikinsu manyan buhunan shinkafa guda biyu da buhunan masara kowannesu.
Adadin magidanta da mata da suka ci moriyar wannan rabo na gwamna Zulum sun kai kimanin mutane 90,000.
Gwamna Zulum a lokacin da yake gudanar da ayyukansa na dare, ya kuma ziyarci babban asibitin domin lura da ayyukan kiwon lafiya na ma’aikatan lafiya.
Ya kuma yi tattaki zuwa Monguno ne tare da jami’an gwamnati da ke aikin gina gidaje sama da 1,000 a garin, da sake gina gidaje da wuraren kiwon lafiya da na ruwa, makarantu da kasuwanni.
Daga cikin jami’an gwamnati akwai kwamishinan sake Ginawa, Gyarawa da Tsugunar da Jama’a na Jihar, Injiniya Mustapha Gubio, Kwamishinonin Shari’a, Barista Kaka Shehu Lawan, Noma, Injiniya Bukar Talba, da sauran masu ruwa da tsaki na Jihar.