Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, ya nada sabon Shehun Bama.
Bayan rasuwar daya daga cikin manyan sarakunan jihar Borno, Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibni Umar Elkanemi, an maye gurbinsa da dansa Umar Ibn Kyari Al’amin Elkenemi a matsayin sabon Shehun Bama.
Marigayin Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibni Umar Elkanemi mai shekara 63, ya rasu ne da yammacin ranar Litinin 27 ga watan Afrilu 2020 a wani asibiti a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
