✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya gwangwaje mutanen Gwoza da tallafin kayan abinci da kudade

Mutanen dai sun rabauta da tallafin kayan abinci da kuma kudade

Gwamnatin Jihar Borno a ranar Asabar ta gwangwaje mutum 27,000 wadanda suka sake dawowa garuruwansu a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar sakamakon rikicin Boko Haram.

Mutanen dai sun rabauta da tallafin kayan abinci da kuma basussuka da tallafi ga masu kananan sana’o’i da ya kai Naira miliyan 150.

Dubban mazauna garin ne dai a yanzu haka suka sake dawowa garuruwan nasu wadanda a baya harin Boko Haram ya daidaita.

Kakakin Gwamna Zulum, Malam Isa Gusau ne tabbatar da raba tallafin a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri.

Ya ce daga cikin adadin, an ware Naira miliyan 100 ga masu kanana da matsakaitan sana’o’i a cikin garin Gwoza, sai Naira miliyan 50 ga garuruwan Izge, Fulka da Liman Kara, duk a cikin Karamar Hukumar ta Gwoza.

A wani labarin kuma, Gwamnan ya kaddamar da wani asibiti mai gadaje 50 a garin Kawuri na Karamar Hukumar Konduga.

Ana sa ran asibitin zai taimakawa mutanen da aka sake tsugunarwa a gidaje sama da 500 da aka sake ginawa a garin.