Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya bukaci a tura jamia’n rusasshiyar runduar ‘yan sanda ta SARS domin taimaka wa yaki da Kungiyar Boko a Jihar.
Da yake karbar bakuncin Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, gwamnan ya ce jami’an SARS sun yi abin a yaba a yaki da Boko Haram a jihar.
- SWAT ta maye gurbin sashen ’yan sandan SARS
- Za a fara horas da ’yan sandan da za su maye gurbin SARS
- Yan banga sun kai wa ofishin ‘yan sanda hari
Gwamnan ya yi kiran ne bayan gwamnan ya yi kiran ne bayan wasu gungiyoyi a jihar sun gudanar da zanga-zangar lumana ta goyon bayan SARS wadda aka yi kwanaki ana zanga-zanga a sassan Najeriya domin a rushe ta.
Zulum said, in Borno state, SARS had made remarkable achievements against Boko Haram.
A jawabinsa Aregbesola ya shaida wa gwamnan cewa ya ziyarci jihar ne domin samun bayanin hakikin yanayin tsaro a jihar.
Ya kuma yaba a Gwamna ZUlum bisa tsayin dakan da ya yi domin ganin an samu tsaro da zaman aminci a jihar Borno.