✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya buƙaci sojoji su samar da sansani a Dajin Sambisa

Kula da tubabbun ‘yan Boko Haram wani ƙalubale ne da ke buƙatar goyon bayan masu ruwa da tsaki.

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya buƙaci sojojin Najeriya da su kafa sansanin soji a dajin Sambisa domin daƙile ayyukan masu tayar da ƙayar baya yadda ya kamata.

Zulum ya bayyana hakan ne a wata ziyarar ban girma da mambobin Kwamitin Majalisar Wakilai kan harkokin soji suka kai masa ranar Laraba a Maiduguri, babban birnin jihar.

Gwamnan ya kuma buƙaci sojojin da su kafa sansanin soji a gaɓar Tafkin Chadi da kuma tsaunin Mandara wanda ke zama mafakar ‘yan ta’adda.

“Akan batun kawo ƙarshen ta’addancin gaba ɗaya, akwai buƙatar gwamnati ta kafa sansanin soji a Sambisa, gaɓar Tafkin Chadi da tsaunin Mandara.”

Ya buƙaci Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta tabbatar da isassun kason makamai don magance matsalar tsaro.

Zulum ya kuma bayyana buƙatar tabbatar da tsaro a Jihar Borno wadda ta yi iyaka da ƙasashe uku, musamman ta fuskar daƙile kwararowar ƙananan makamai da ke ƙara rura wutar matsalar tsaro a Arewacin ƙasar.

Ya ƙara jaddada ƙudurinsa na tallafa wa sojoji a fagen yaƙi da ta’addanci, yana mai cewa kawo yanzu tubabbun ‘yan Boko Haram 190,000 ne suka miƙa wuya ga mahukunta.

A cewar Zulum, kula da ɗimbin tubabbun ‘yan Boko Haram wani ƙalubale ne da ke buƙatar goyon bayan masu ruwa da tsaki.