✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zulum ya bai wa sojojin da suka jikkata tallafin kudi

Ya yaba wa sojojin kan kare martabar Jihar Borno da kasa baki daya.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da sakin naira miliyan 10 a matsayin tallafi ga sojojin da suka samu raunuka a fadace-fadacen da aka yi a jihar.

Wannan tallafin kamar yadda wakilinmu ya ruwaito sauke nauyin alkawari ne da Gwamna Zulum ya yi watanni biyu da suka gabata a wajen bikin murnar Sallah da Babban Hafsan Sojin Kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya shirya.

Kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na Jihar Borno, Farfesa Usman A Tar tare da Mataimakin Babban Sakataren Fadar Gwamnati, Barista Mustapha Ali Busuguma ne suka kai kyautar Gwamnan ga babban kwamandan runduna ta 7, Manjo Janar Peter Malla a hedikwatar 7 Div da ke birnin Maiduguri.

“Mun zo nan ne domin cika alkawarin da mai girma Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi.

“Ana iya tuna cewa Gwamnan ya zo ne a ranar Sallah domin wani biki, inda ya bayyana kudirin gwamnatin Jihar Borno na bayar da gudunmawar Naira miliyan 10 ga dakarun da suka jikkata, musamman saboda kwazonsu fagen daga.”

Gwamnan ya kuma bayyana kudirinsa na ci gaba da tabbatar da goyon baya wajen bayar da tallafin kayan aiki da inganta jin dadin sojoji.

Kazalika, ya kuma yaba wa sojojin kan kare martabar yankin Najeriya da kuma tabbatar da zaman lafiya a Borno.

Da yake karbar tallafin, kwamandan runduna ta 7 GOC, Manjo Janar Peter Malla ya nuna jin dadinsa ga Gwamna Zulum bisa wannan karamci.

“A madadin kwamandan rundunar OPHNK  muna maraba da zuwanku.

“Sannan kuma ina nuna godiyarmu ga mai girma gwamna kan yadda yake tallafa wa sojoji a koyaushe,” in ji Manjo Janar Malla.

Manjo Peter ya ba da tabbacin samun ci gaba da dorewar zaman lafiya da ake samu a Borno ta hanyar kawar da ragowar masu tada kayar baya.